Sojoji Sun Ceto Yarinya Ƴar Shekara 13, Sun Hallaka Ƴan Ta’adda A Dajin Zamfara

[ad_1]

Sojojin Atisayen FANSAR YAMMA sun ceto wata yarinya ƴar shekara 13 mai suna Halira Ibrahim, daga hannun ƴan ta’adda a Dajin Sububu da ke jihar Zamfara, yayin wani ƙoƙarin wargaza maɓoyar ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan.

Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Atisayen FANSAR YAMMA, Kyaftin David Adewusi, ya fitar ya bayyana cewa sojojin da ke ƙarƙashin ɓangare na 2 na Runduna ta 8, sun kai farmaki kan wuraren da aka gano ƴan ta’adda a ƙauyukan Indulumu da Ruduno, inda suka fafata da su tare da musayar wuta mai tsanani.

  • Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram 2, Sun Kama Wasu 8 A Borno
  • Sojoji Sun Nemi Ƴan Sokoto Su Miƙa Ragowar Ɓaraguzan Bam Ɗin Amurka

Adewusi ya ƙara da cewa, a yayin wannan fafatawa, sojojin sun yi nasarar ceto yarinyar da aka sace, tare da hallaka ƴan ta’adda da dama, inda suka ƙwato bindigogi 28 ɗauke da harsasai da kayan sojoji da kuma babura.

Ya bayyana cewa sojojin sun ci gaba da aikin kakkaɓe dajin, inda suka gano tare da lalata sansanonin ƴan ta’adda da gine-ginen da suke kula da marasa lafiyarsu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *