Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa A Ayyukan Hukumar IMO

[ad_1]

Babban sakataren hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta kasa da kasa ko IMO Arsenio Dominguez, ya ce kasar Sin muhimmiyar memba ce a hukumar ta IMO, kuma za ta ci gaba da shiga a dama da ita a muhimman ajandojin da hukumar ke fuskanta cikin shekaru dake tafe.

Dominguez, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudana jiya Juma’a a helkwatar hukumar ta IMO dake birnin Landan, inda ya gabatar da muhimman ayyukan da hukumar za ta gudanar a shekarar nan ta 2026, tare da amsa tambayoyin da manema labarai suka gabatar.

Yayin da yake amsa tambaya daga wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, Dominguez ya ce Sin na gudanar da tashoshin jiragen ruwa mafiya girma a duniya, kuma a yanzu haka ita ce kasa dake kan gaba a duniya wajen kera jiragen ruwa.

Jami’in ya kara da cewa, ci gaban kasar Sin a fannin fasaha, da karkatar ta ga ayyuka marasa gurbata muhalli, da kokarinta na fadada nagarta a sassan kare hadurra, da tsaro da ayyuka tsakanin jirage da tashoshi, dukkanin su abubuwa ne masu tasiri ga ayyukan IMO, kuma muhimman bangarori ne cikin bayanan da ake bukata wajen gudanar da ayyukan hukumar yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *