23 ga Janairu ita ce “Ranar Cin Amana ta Duniya” — Kwankwaso

[ad_1]



Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana ranar 23 ga watan Janairu a matsayin “Ranar Cin Amana ta Duniya.”

Kwankwaso, ya bayyana haka ne bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar NNPP a ranar 23 ga watan Janairu, 2026.

An jima ana raɗe-raɗin gwamnan ƙoƙarin ficewa daga jam’iyyarsu ta NNPP tare komawa jam’iyyar APC.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano, Kwankwaso ya ce ayyana ranar ya samo asali ne daga maganganun da ya gani a kafafen sada zumunta.

Wasu mutane sun bayyana ficewar gwamnan daga jam’iyyar NNPP a matsayin cin amana.

Kwankwaso, ya ce wani saƙo da aka wallafa a kafafen sada zumunta ne ya ɗauki hankalinsa, inda aka ba da shawarar a riƙa tunawa da ranar 23 ga watan Janairun kowace shekara a matsayin “Ranar Cin Amana ta Duniya”.

Ya ce a matsayinsa na jagora, yana goyon bayan wannan shawara.

Ya ƙara da cewa daga yanzu za a riƙa gudanar da wasu bukukuwa na musamman a wannan rana domin tunatar da mambobin jam’iyyar abin da ya faru.

Tun da farko, Gwamna Abba ya sanar da ficewarsa daga NNPP, inda ya ce rikice-rikicen cikin gida da matsalolin shugabanci ne suka sa shi yanke wannan shawara.

Magoya bayan gwamnan sun ce matakin nasa dabarar siyasa ce mai kyau, wadda za ta kawo masa kusanci da Gwamnatin Tarayya.

Amma magoya bayan Kwankwaso sun bayyana matakin a matsayin cin amana da ka iya ƙara dagula siyasar Jihar Kano.

A gefe guda kuwa, magoya bayan APC sun yi maraba da ficewar gwamnan, inda suka bayyana cewa hakan zai ƙara ƙarfin jam’iyyarsu a Kano.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *