Sarkin Zuru ya gana da Ministan tsaro kan matsalar tsaro a Jihar Kebbi

[ad_1]



Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya karɓi baƙuncin Sarkin Zuru Alhaji Sanusi Mikailu Sami Sami Gomo III a ofishinsa da ke Abuja inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi a rashin tsaro a yankin Zuru da Jihar Kebbi.

Ganawar ta samu halartar ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Masarautar Zuru, Kabir Ibrahim Tukura, da sauran ’yan majalisar Sarki ciki har da Janar Ishaya Bamaiyi da kuma Manjo-Janar Muhammadu Magoro Galadiman Zuru.

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa sha’anin tsaro tare da katse ayyukan ’yan ta’addan da suka addabi masarautar Zuru da jihar Kebbi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *