Ma’aikatan KEDCO Sun Dakatar Da Yajin Aiki

[ad_1]

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya sanar da dakatar da yajin aikin da ma’aikatansa suka shiga, biyo bayan cimma matsaya tsakanin shugabancin kamfanin da ƙungiyoyin ƙwadago. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Sadarwa na Kamfanin, Sani Bala Sani, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, an cimma wannan matsaya ne bayan “tattaunawa mai ma’ana da shawarwari na zahiri” tsakanin dukkan ɓangarorin da abin ya shafa. An bayyana cewa ƙoƙarin haɗin gwuiwa na Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), da Hukumar BPE, da kamfanin Future Energies Africa (FEA) da Ma’aikatar Wuta da Makamashin zamani mai Ɗorewa ta Jihar Kano ne suka taimaka wajen warware matsalar.

  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
  • Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta: Kotu Ta Tsare Maƙwabta 2 Kan Bayar Da Bayanan Ƙarya A Kano

KEDCO ta ce warware batutuwan da suka gada kamar bashin fansho, da albashin ma’aikata da sauran alawus-alawuswanda suke suka kasance babban abin da ta fi maida hankali a kai tun bayan shigar FEA a matsayin masu zuba jari. Kamfanin ya ƙara da cewa yana sa ran shirin da ya fara zai taimaka wajen warware waɗannan matsaloli a nan gaba.

Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma, akwai biyan bashin albashin wata na 13 (bonus) na Naira miliyan 150 da kuma bashin kuɗin tantance aiki na Naira miliyan 20 daga shekarun baya, wanda ya kai jimillar naira miliyan 170. Haka kuma, kamfanin ya yi alƙawarin biyan bashin albashin wata na 13 na shekarar 2025, wanda ya kai Naira miliyan 174, a zagayen albashin Fabrairu 2026.

Kamfanin ya kuma jaddada cewa an amince da tsarin tattaunawa mai faɗi da ta haɗa NLC, da ƙungiyoyin ma’aikatan wutar lantarki da kwamitin daraktocin KEDCO domin magance sauran matsaloli. Sanarwar ta ƙare da cewa an dawo da ayyuka kamar yadda aka saba a dukkan yankunan da kamfanin ke yin aiki, tare da tabbatar wa abokan hulɗa da al’umma cewa za a ci gaba da inganta samar da wutar lantarki da kyautata hulɗar aiki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *