Me Ya Sa Masu Koyarwa ‘Yan Asalin Ingila Ba Sa Iya Lashe Kofin Premier?

[ad_1]

Wasu suna ganin zuwan Liam Rosenior Chelsea zai ba shi damar sauya alƙiblar tarihin gasar Premier League ga manyan masu horarwa ƴan Ingila.Tun bayan yi wa Premier League kwaskwarima kusan shekara 34 da suka wuce, ɗaya daga cikin manyan abubuwan ban mamaki a gasar shi ne da aka kasa samun kociya ɗan Ingila da ya lashe gasar.

Mai horarwa Howard Wilkinson, wanda yanzu yake da shekara 82 kuma dattijo a harkar ƙwallon ƙafa, shi ne ɗan Ingila na ƙarshe da ya ɗauki kofin tare da Leeds United a kakar wasa ta 1991 zuwa 1992, amma a lokacin ana kiran gasar da First Division ne.

  • Sauyin Da Sin Ta Yi Zuwa Samun Ci Gaba Mai Inganci Ya Kawo Lumana Ga Tattalin Arzikin Duniya – Shugaban WEF
  • Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi

Tun daga wancan lokaci, masu koyarwa 12 ne suka jagoranci ƙungiyoyinsu zuwa ɗaukar Premier League, amma babu ko ɗaya ɗan ƙasar Ingila daga ciki. Kuma daga nasarorin da aka samu ɗan ƙasar Scotland, Sir Aleɗ Ferguson ne kan gaba mai Premier League 13 a Manchester United da kuma ɗan ƙasar Sifaniya, Pep Guardiola mai shida a Manchester City.

Mai koyarwa Rosenior, mai shekaru 41, shi ne koci na huɗu ɗan Ingila a halin yanzu a gasar Premier League, bayan da ya koma Chelsea daga Strasbourg, sauran sun haɗa da Sean Dyche na Nottingham Forest da Eddie Howe na Newcastle United da kuma Scott Parker na Burnley. Michael Carrick ya karvi aikin jan ragamar Manchester United bayan korar Ruben

Amorim, amma na wucin-gadi ne kawai zuwa ƙarshen kakar wasan bana. Wannan ƙarancin adadin ƴan Ingila masu horarwa a Premier League ya yi ƙasa sosai matuƙa idan aka kwatanta da manyan gasanni biyar na Turai wajen wakilcin ƴan ƙasa a gasa.

A Italiya, koci 16 daga cikin 20 a gasar ƴan Italiya ne, a Sifaniya, 11 daga cikin 20 ƴan Sifaniya ne, a Jamus, 12 daga cikin 18 ƴan Jamus ne; yayin da a Faransa, 10 daga cikin 18 ƴan Faransa ne.

Idan aka haɗa da kociyoyin riƙon ƙwarya da na wucin gadi, an samu 92 waɗanda ba ƴan Birtaniya ko Ireland ba a tarihin Premier League. A halin yanzu, teburin gasar na Premier League, Arsenal kan gaba tare da mai horarwa, Mikel Arteta, sai Manchester City ta biyu ƙarƙashin Pep Guardiola, sannan Aston Villa ta uku tare da Unai Emery — dukkaninsu ƴan ƙasar Sifaniya ne.

To, me ya sa Premier League ta gagari kociyoyin Ingila haka, kuma shin akwai wanda zai iya kawo ƙarshen wannan kasa lashe kofin?

Zamanin da Ferguson ya yi da sauran kociyoyin ƙasashen waje Tun bayan da aka canja tsarin gasar Premier League a kakar 1992–93 ta zo daidai da lokacin da Ferguson ya kawo ƙarshen shekaru 26 da Manchester United ta kasa lashe lig, wanda sai da ya ɗauki 13 tun bayan da ya koma ƙungiyar, har yanzu ba a samu kociyan da ya yi wannan ƙwazon ba.

A kuma lokacin Aston Villa, ƙarƙashin jagorancin Ron Atkinson, ta kammala kakar a matsayi na biyu. Hakan ya kasance ɗaya daga cikin damar da wani ɗan Ingila ya lashe Premier League.

Wani ɗan Scotland, Sir Kenny Dalglish, ya takawa Ferguson burki, lokacin da ya jagoranci Blackburn Rovers zuwa lashe Premier League a kakar 1994–95, kafin nan Premier League ta zama matattarar manyan masu koyarwa daga Turai.

An tarbi Arsene Wenger da kanun labarai da cewa “Arsene wa?” lokacin da ya koma Arsenal daga ƙungiyar, Nagoya Grampus Eight ta Japan ranar 30 ga Satumba, 1996.

Kafin zuwan Wenger, koci biyu ne kacal daga ƙasashen waje, Osvaldo Ardiles da Ruud Gullit, da suka tava horarwa a Premier League.

Wenger ya zama mutummin da ya sauya fasalin gasar baki ɗaya, saboda sabbin tsare-tsare da dabara da hangen nesa a lokacin da ya gudanar da aikinsa. Ya lashe kofin lig uku — ciki har da kakar da aka yiwa laƙabi “The Invincibles” a 2003 zuwa 2004 inda Arsenal ba ta yi rashin nasara

ba a kakar gabaki ɗayanta — sannan ya ɗauki kofin FA, bakwai (shi ne kan gaba a wannan tarihi), da kuma Charity/Community Shieldn guda shida. Haka kuma ya ɗauki lig da FA Cup a kaka ɗaya kuma sau biyu a shekarar 1998 da kuma 2002.

Me Ya Sa Ƙwazon Masu Koyarwa Ƴan Ingila Yake Yin Ƙasa?

Chelsea ta fara farfaɗowa ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho, wanda ya koma Ingila daga Porto a shekarar 2004 a matsayin wanda ya lashe gasar Kofin zakarun Turai, inda nan take ya kawo ƙarshen kasa lashe kofi da ƙungiyar ke fama tun bayan 1955.

Wannan ne ya buɗe ƙofa ga shigowar masu horarwa da suke lashe manyan kofuna ƴan ƙasar waje, irin su ƴan Italiya da ya haɗa da Carlo Ancelotti da Antonio Conte da Roberto Mancini da Claudio Ranieri da ɗan Chile, Manuel Pellegrini, sannan ɗan Jamus Jurgen Klopp a Liverpool, wanda daga baya ɗan ƙasar Holland Arne Slot ya biyo baya.

Shin kociyoyi ƴan ƙasar Ingila suna da dama kuwa?

Yawan lokutan da ake bai wa masu koyarwa ƴan Ingila a manyan ƙungiyoyin Premier League yanzu ya ragu sosai, duk da cewa Newcastle United ce ke amincewa da koci, ƴan Ingila tun bayan Ron Atkinson da ya ƙare a mataki na biyu, sai lokacin da suka bayar da tazarar maki 12 daga baya Manchester United ta sha gabanta a 1995 zuwa 1996.

Sai kuma yanzu Eddie Howe da yake horar da ƙungiyar St James Park. Newcastle tana aiki da kociyoyin Ingila cikin kaka tara a Premier League fiye da idan ka kwatanta da Tottenham da Aston Villa da sauran su.

Tsohon kocin Tottenham, Harry Redknapp, ya ƙare a matsayin koci ɗan Ingila mafi matsayi sau biyar a Premier League, ya zarce Howe wanda ya yi hakan sau huɗu, sai Sam Allardyce da Sir Bobby Robson, kowannensu sau uku.

Rosenior ya samu damar zuwa Chelsea ta wata sabuwar hanya, inda aka ba shi aikin ta tsarin horar da ƙungiyar Chelsea saboda ƙungiyar tana daga cikin mallakin kamfanin BlueCo.

Da Rosenior, wanda Hull City ta sallama a watan Mayun 2024 kafin daga bisani ya bar Strasbourg yana matsayi na bakwai a Ligue 1, ya samu wannan dama a Chelsea ba tare da kasancewa cikin wannan tsarin ba?

Tony Pulis, wanda ya tava fafatawa da manyan kociyoyin Turai a lokacin da yake Stoke City, ya yi imanin cewa akwai babban dalili guda ɗaya da ya sa jerin manajojin da suka lashe Premier League bai ƙunshi sunan wani ɗan Ingila ba.

Ya ce “Zan yi tambaya ne kawai, kociyan Ingila nawa ne suka tava jagorantar manyan ƙungiyar a cikin shekaru 25 da suka gabata? Wannan ne dalilin da ya sa babu wani koci ɗan Ingila da ya tava lashe Premier League.

Ya ci gaba da cewa “Idan ka duba ƙungiyoyin da suka lashe kofuna da dama a wannan lokaci, ƙungiyoyin suna nan, ƴan wasan suna nan masu iya lashe kofuna, amma galibi kociyoyi ƴan ƙasashen waje ne ke zavar ƴan wasan. Idan ba ka da ƙungiya mafi kyau da kuma ƴan wasa mafi nagarta, ba za ka iya lashe Premier League ba.”

Sai dai Gary O’Neil, wanda ya gaji Rosenior a Strasbourg bayan da ya tava horar da AFC Bournemouth da Wolverhampton Wanderers, yana da ra’ayi daban. Ya ce: “Abu ne mai sauƙi a ce kociyoyin Ingila ba sa samun dama, amma ban ga wannan a matsayin cikakkiyar gaskiya ba.

Ya ce yana ganin Premier League ita ce gasar ƙwallon ƙafa mafi kyau a duniya, wadda ke da kuɗi mafi yawa. Ya ci gaba da cewa duk wani koci ɗan Ingila, dole ne ya cancanci wannan dama. Ba wanda ake bai wa manyan muƙamai a matsayin kyauta ba.

Dole ne sai ya cancanta, kuma wasu daga cikin masu horarwa da suka zo Ingila suka yi nasara suna da ƙwarewa mai matuƙar girma.”

Wane koci ne ɗan Ingila zai fara lashe kofin Premier League?

Sabon mai koyar da ƴan wasan Chelsea, Rosenior ya fi dacewa saboda damar da yake da ita a hannunsa, hazaƙa da kuma yadda Chelsea ke shirye-shiryen zuba jari — amma wasu suna da fata ga Eddie Howe da kuma Frank Lampard.

Howe ya lashe kofin cikin gida a karon farko cikin shekaru 70 na farko cikin shekaru 56, lokacin da suka doke Liverpool a wasan ƙarshe a Carabao Cup a kakar da ta gabata. Haka kuma ya kai su gasar Champions League karo na biyu.

Aikin koyarwa da Frank Lampard ke yi na farfaɗowa cikin nasara a Coventry City, waɗanda suke na ɗaya a gasar Championship, bayan da ya horar da Chelsea sau biyu, haka kuma a Derby County da Everton.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *