Sin: Japan Ba Ta Cancanci Neman “Zaunanniyyar Kujera A MDD” Ba
[ad_1]
Mukaddashin wakilin zaunanniyyar tawagar Sin dake MDD Sun Lei, ya ce Japan ba za ta iya sauke nauyin shimfida zaman lafiya da tsaro a kasa da kasa ba, kuma ba za ta iya samun amincewar al’ummar kasa da kasa ba, don haka ba ta cancanci neman zama memban dindindin na kwamitin sulhu na MDD ba.
Sun Lei, ya bayyana haka ne jiya, yayin jawabi a gun muhawara karon farko tsakanin gwamnatocin kasashe daban-daban da kwamitin sulhu, wanda babban zauren MDD na 80 ya gudanar game da yi wa kundin tsarin MDD kwaskwarima.
A cewar wakilin na Sin, shekaru 80 da suka gabata, an yanke hukunci mai tsanani kan masu laifin yaki na Japan a Tokyo, matakin da ya tabbatar da adalcin kasa da kasa, kuma wannan ya kasance gargadi mai karfi ga duk wani yunkurin dawo da ra’ayin amfani da karfin soja da sake fadada mulkin mallaka. Duk da haka, ba a kawar da masu ra’ayin nuna karfin soja gaba daya a Japan ba, a maimakon haka sun canza fuska, suna girma a asirce. Ya ce masu tsatsauran ra’ayi na Japan suna yunkurin daukaka laifufukan yakin mahara na kasar, suna musanta kisan kiyashi na Nanjing da tilasta wa mata shiga karuwanci, da tilasta wa jama’a yin aiki da sauran laifuffukan da aka aikata a tarihi. Suna kuma yunkurin murguda gaskiya cikin littattafan tarihi. Ya ce da yawa daga cikin shugabannin Japan na yanzu, sun kai ziyara wurin ibada na Yasukuni, wanda ya kasance alamar ruhin karfin soja na Japan.
Sun Lei ya ce, daga kalamai mara dacewa na firaministar Japan mai ci Takaichi Sanae game da yankin Taiwan da barazanar nuna karfin soja kan Sin, zuwa maganganun goyon bayan makaman nukiliya da manyan jami’an Japan suka furta, har ma da ikirarin gyara “ka’idojin uku na kawar da nukiliya a Japan”, sun bayyana cikakken tsatsauran ra’ayin Japan na dawo da ra’ayin amfani da karfin soja, wanda ke haifar da sabon barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin har ma na duk fadin duniya. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link