Sace Masu Ibada: Ashiru Ya Caccaki Gwamnatin Kaduna Kan Rashin Iya Shugabanci


Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 a Jihar Kaduna, Isa Mohammed Ashiru, ya soki Gwamnatin jihar kan sace masu ibada 177 a wasu coci guda uku a Kurmin Wali, Ƙaramar Hukumar Kajuru.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ashiru ya bayyana lamarin a matsayin rashin iya shugabanci da mulki.

  • He Lifeng Ya Halarci Taron WEF Tare Da Ziyartar Kasar Switzerland
  • 2027: Yunƙurin Sauya Shettima A Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Ɓaraka Zai Janyo A APC – Matasa

Ya ce sace mutanen ya nuna cewa gwamnati ta kasa gudanar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyi.

Ashiru ya kuma soki Gwamna Uba Sani kan musanta sace mutanen da aka yi da farko, duk da rahotannin ɓacewar mutanen yankin.

Ya zargi gwamnatin jihar da rashin ƙwarewa da tausayi.

Ya ce duk wata gwamnati da ba za ta iya kare al’umma, coci, ƙauyuka, hanyoyi da gonaki ba, ba za a iya yadda da makomar jihar a hannuta ba.

A ƙarshe, Ashiru ya buƙaci al’ummar Kaduna da su nemi ba’asi daga shugabanni, tare da kira a sauyi gabanin zaɓen 2027, yana mai cewa Jihar Kaduna ta cancanci shugabanci na gari, gaskiya da jajircewa.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *