Kayayyakin Sola Kirar Kasar Sin Sun Bunkasa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta A Nahiyar Afrika

[ad_1]

An alakanta karuwar amfani da makamashi mai tsafta a fadin nahiyar Afrika, da samun kayayyakin samar da lantarki daga hasken rana na sola masu inganci da araha na kasar Sin.

Wani dan kasuwa na kasar Kenya Georg Pflomm, wanda shi ne manajan cibiyar bunkasa makamashi da muhalli da tattalin arziki mai dorewa na kamfanin AHK Services a gabashin Afrika ne ya bayyana hakan. Yana mai cewa, kayayyakin sola na kasar Sin na bunkasa amfani da makamashi da wadatarsa a nahiyar dake da burin ganin raguwar fitar hayakin carbon.

Ya ce a shekarun baya-bayan nan, galibin masu ruwa da tsaki a harkar sola ’yan kasar Sin ne. Kuma kasar na da kamfanoni da dama dake samar da kayayyakin sola masu inganci. Ya kara da cewa, kasar Sin ta zama mai matukar muhimmanci a fannin tsarin samar da kayayyakin sola a duniya, lamarin dake amfanawa kasashen Afrika dake son bunkasa amfani da makamashi mai tsafta a turakunsu na lantarki. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *