Ko Fir’auna bai yi zaluncin kashe uwa da ’ya’yanta gaba ɗaya ba — Sheikh Daurawa
[ad_1]
Fitaccen malamin addinin Islama a Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya koka kan tsananin taɓarɓarewar tsaro, yana mai cewa a wannan zamani mutane ba su da aminci hatta a cikin gidajensu.
Ya bayyana hakan ne cikin wani sakon bidiyo yayin da yake martani kan kisan wata mata, Fatima, da ’ya’yanta shida da wasu matasa suka yi a yankin Dorayi Chiranchi, Kano.
Sheikh Daurawa, wanda shi ne Shugaban Hukumar Hisbah na Kano, ya ce lamarin ya girgiza shi matuƙa har ya kasa barci, yana mai bayyana hotuna da bidiyon mummunan lamarin da ya gani a matsayin abin firgitarwa.
Ya siffanta kisan da ya bayyana a matsayin ta’addanci da abin da bai taɓa faruwa ba a tarihi, yana mai cewa ko Fir’auna bai kai wannan zalunci ba.
“Idan na tuna tarihin Fir’auna, sai na ga ai ko shi (Fir’auna) bai kashe mata ba; maza ya kashe. Ko a zamanin Jahiliyya, ba a yi irin wannan zaluncin ba na kashe uwa da ’ya’yanta gaba ɗaya ba.
Ya jaddada cewa rashin tsaro ya kai matakin intaha na ƙololuwa, yayin da ya ce ana kai hari kan iyalai a lokacin da masu gidan ba su nan.
Daurawa ya ɗora laifin yawaitar laifuka kan rashin tarbiyya da sakacin al’umma, inda ya bayyana cewa masu aikata laifuka ’ya’ya ne a cikin wannan al’umma da suka aka bari suka faɗa shaye-shaye da rashin aikin yi.
Shehin malamin ya bayyana cewa yadda ake kai hare-haren ta’addanci a wannan lokaci har a samu masu kashe iyayensu ko kuma ma’auratan da ke kashe abokan zamansu ko ’yan uwa masu zubar da jinin juna, lamari ne da ya kamata ya ɗaga hankalin duk wani mai imani.
Shugaban Hukumar Hisbar ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da kama duk wasu masu hannu a kisan tare da tabbatar da adalci.
Haka kuma, ya ankarar da gwamnonin jihohi kan jinkirin rattaba hannu kan hukuncin kisa ga waɗanda aka samu da laifin kisan kai, yana gargaɗin cewa duk wanda ya yi jinkiri zai ɗauki alhakin hakan a Lahira.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link