Hainan Ta Karbi Karin Masu Bude Ido Daga Ketare

[ad_1]

A yau Litinin, ofishin yada labarai na lardin Hainan ya gudanar da taron manema labarai don bayyana ci gaban da aka samu a watan farko na aiwatar da manufar kafa hidimar “kwastam mai zaman kanta a duk fadin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin” .

An bayyana cewa, a watan farko na aiwatar da wannan manufa a Hainan, an samu bunkasuwar sha’anin yawon bude ido a bangaren karbar baki daga ketare, inda aka samu kyakkyawan ci gaba. A watan Disamba na shekara ta 2025, lardin Hainan ya karbi baki masu yawon shakatawa da suka kwana a wurin har sau 773,000, wanda ya karu da kashi 59.5 cikin 100 idan aka kwatanta da shekara ta 2024. Yawan masu bude ido da Sin ta karba daga kasar Rasha da kasashen dake kudancin gabashin Asiya, da yankunan Hong Kong, da Macau, da Taiwan, sun ci gaba da karuwa a hankali, haka ma yawan masu bude ido daga yankuna masu nisa kamar Turai, Amurka, Austriliya da New Zealand, da shi ma ya nuna kyakkyawan ci gaba. Yawan kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe a nan kasar Sin shi ma ya karu, inda ya kai dala miliyan 141.4 a watan Disamba na shekara ta 2025, wanda ya karu da kashi 63 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *