Adalci: Gwamnatin Kano Ta Karɓi Ragamar Shari’ar Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓe ragamar shari’ar kisan uwa da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, domin tabbatar da an yi adalci.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, yana bayyana matukar mamaki da bakin ciki game da lamarin, wanda ya bayyana a matsayin “mummunan aiki” da kuma mummunan cin zarafin ɗan Adam da kuma rashin mutunta doka.
- Sojoji Sun Daƙile Harin Jirgi Maras Matuƙi Na Ƴan Boko Haram A Borno
- Ƴan Nijeriya Sun Cire Tiriliyan ₦36.3 Ta ATM Cikin Watanni 6 Duk Da Ƙarin Kuɗin Caji — CBN
“Na yi matukar mamaki da bakin ciki da kisan gillar da aka yi wa wannan baiwar Allah da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano. Irin wannan mummunan aiki babban cin zarafi ne ga dan Adam da kuma rashin mutunta doka,” in ji Maude.
Ya bayyana cewa a karkashin umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ofishinsa ya ɗauki alhakin ci gaba da shari’ar don tabbatar da cewa an yi adalci.
Babban Lauyan ya yaba wa Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano saboda abin da ya bayyana a matsayin martanin gaggawa da kuma nuna ƙwarewa a aiki da ta kai ga kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.
[ad_2]
Source link