AFCON 2025: Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Morocco
[ad_1]
Yau Lahadi ne za a buga wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) 2025, inda manyan kasashe biyu na nahiyar Afirka, Morocco mai masaukin baki da Senegal, za su kara domin lashe kofin. Morocco na fatan kawo karshen shekaru kusan 50 ba tare da daukar kofin ba, yayin da Senegal, karkashin jagorancin tauraron dan kwallo Sadio Mané, ke neman lashe gasar a karo na biyu a tarihinta.
Za a buga wasan ne da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat. Ana sa ran fiye da magoya baya 69,000 za su cika filin domin goyon bayan kasashensu, musamman tawagar Morocco da ke karkashin jagorancin gwarzon dan kwallon nahiyar Afirka na bana, Achraf Hakimi.
- Duk Da Rashin Nasara A Hannun Morocco, BUA Ya Bai Wa Super Eagles Kyautar Dala 500,000
- AFCON 2025: Morocco, Senegal Da Mali Sun Tsallaka Zuwa Zagayen Kwata Fainal
Gasar AFCON ta bana ta kasance ta musamman, kasancewar an fara ta ne a karshen shekarar 2025, kuma akwai yiwuwar ta zama karo na biyu a jere da kasar da ke karbar bakunci za ta lashe gasar. A shekarar 2024, Ivory Coast ce ta lashe kofin bayan doke Najeriya a wasan karshe a gaban magoya bayanta a birnin Abidjan.
Morocco ta yi fice a fagen kwallon duniya bayan zama kasa ta farko daga Afirka da ta kai matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022, inda ta kai matsayi na 11 a jadawalin FIFA. A bangaren Senegal kuma, suna neman maimaita nasarar da suka samu a 2022, lokacin da Sadio Mané ya zura bugun fenariti a wasan karshe da suka doke Masar a birnin Yaounde.
[ad_2]
Source link