Sarkin Musulmi ya buƙaci a soma laluben watan Sha’aban




Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci a fara duba jinjirin watan Sha’aban na shekarar Hijira 1447 daga gobe Litinin, 29 ga watan Rajab, wanda ya yi daidai da 19 ga watan Janairu, 2026.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini a Masarautar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya raba wa manema labarai.

Sarkin wanda ya yi kira ga al’ummar Musulmin Nijeriya da su fara duban jinjirin watan na Sha’aban, ya buƙaci duk wanda ya gani da ya gaggauta sanar da Majalisar Sarkin Musulmi domin sanar da al’umma.

Har ila yau, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya taimaki al’umma a wannan aiki na ibada da suke gudanarwa.

Watan Sha’aban na da matuƙar muhimmanci a Musulunci, kasancewarsa watan da ke gab da watan Ramadan — watan ibada da azumi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *