Gwamnatin Kano ta musanta dakatar da harkokin tafiyar da mulki




Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da harkokin tafiyar da mulki na jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai ga Sakataren Gwamnatin Jihar, Musa Tanko Muhammad, ya fitar a ranar Juma’a.

Gwamnatin ta ce umarnin na wucin-gadi ne kuma an ɗauke shi ne domin bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗen gwamnati.

Sanarwar ta bayyana cewa an bayar da umarnin dakatar da tura takardu zuwa ofishin gwamna ne a ƙarshen watan Disamban 2025, lokacin da kasafin kuɗin shekarar 2024 ya ƙare, yayin da kasafin kuɗin shekarar 2025 ke gaban Majalisar Dokokin Jihar.

Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin hana kashe kuɗaɗen da doka ba ta amince da su ba, domin babu yadda za a amince da kashe kuɗi ba tare da ingantaccen kasafi ba.

Ta ƙara da cewa muhimman ayyuka kamar tsaro, kiwon lafiya, ilimi da tsaftar muhalli na ci gaba da gudana ba tare da wata tangarda ba.

Gwamnatin ta bayyana cewa iƙirarin cewa harkokin gudanar da mulki sun tsaya ba gaskiya ba ne.

Ta ce umarnin wani mataki ne da aka ɗauka domin ƙarfafa bin ƙa’ida da gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

Ta kuma tabbatar wa al’umma cewa za ta yi ƙarin bayani bayan kammala nazari kan harkokin gudanarwa da ake yi a halin yanzu.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *