Shin Alonso Ya Cancanci Kora A Real Madrid?

[ad_1]

Za a iya cewa an daɗe ana tsammanin irin matakin da ƙungiyar Real Madrid za ta ɗauka a kan Xavi Alonso, mai koyarwar da aka yi tunanin zai jima yana koyar da babbar ƙungiyar ta Nahiyar Turai.

Daman an ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kyian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya.

  • Xabi Alonso Ya Ajiye Aiki A Real Madrid Bayan Cimma Matsaya
  • Real Madrid Ta Shiga Halin Damuwa Bayan Wasanni Uku Ba Tare Da Nasara Ba

A cikin bidiyon an ga yadda Xavi Alonso ya buƙaci Mbappe ya tsaya, amma sai ɗan wasan ya dage, sai kuma aka ga daga ƙarshe Alonso ya haƙura, inda ya bi muradin Mbappe suka fice daga filin.

Lamarin da ya hana ƴan wasan yi wa tawagar Barcelona tsayuwar girmamawa domin karɓar kofin bayan lashe shi a ƙarshen mako. Masana ƙwallon ƙafa da dama suna kallon hakan a matsayin rashin girmama wasanni, wani abu da ba a taɓa alaƙanta wa da Alonsa ba.

Haka kuma hakan ya nuna cewa ƴan wasan ne ke juya ƙungiyar ba kocin ba. Sakamakon hakan ne kuma Ɗabi Alonso ya sauya tunani game da aikinsa, amma wannan ba ritaya ba ce, ba abu ne kuma da ya shiryawa ba domin ba a yi tsammanin Alonso zai bar Madrid ba wata bakwai da rabi bayan fara horar da ƙungiyar da ya bugawa ƙwallo a baya.

A cikin sanarwar da Real Madrid ta fitar a hukumance, ƙungiyar ta bayyana rabuwa da kocin da cewa an yi hakan ne bisa amincewa da juna, amma kuma rabuwa ce da babu makawa.

Me Ya Sa Real Madrid Ta Rabu Da Alonso Wataƙila bayan rashin jituwa mai yawa da ta riƙa samu da kocinta kan dabaru da salon wasa, na tsawon watanni, a ranar Litinin da maraice ne, hukumar gudanarwar ƙungiyar ta yi wani zama da nufin raba gari da Alonso.

An yi masa bayanai masu gamsarwa, amma kuma masu harshen damo da suka haɗa: Kasa aiwatar da dabarun da suka kai shi ga nasara a ƙungiyar Bayer Leɓerkusen. Ƙarfin ƙungiyar bai kai yadda take buƙata ba. Ƴan wasa sun kasa ƙara ƙoƙari’. Wasan da suke bugawa bai nuna nasa ba ne.

An kuma lissafo rashin narasar da ya samu a ƙungiyar da suka haɗa da: Doke ƙungiyar ta PSG ta yi a wasan kusa da ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na Ƙungiyoyi da kuma ci 5-2 da Atletico Madrid ta yi wa ƙungiyar a Gasar La Liga.

To amma yanzu haka Madrid na mataki na takwas a teburin Gasar Zakarun Turai, gasar da ke fayyace ƙarfin ƙungiyar. Haka kuma sun kai matakin gaba a Gasar Copa del Rey, kuma suna mataki na biyu a teburin
La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya, kuma sun doke Barca a lokacin da suka kara cikin watan Oktoba.

Wace Irin Matsala Alonso Ya Fuskanta A Madrid Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa dama shugaban ƙungiyar Florentino Perez ba ya son
aikinsa a ƙungiyar. an ba shi shawarar ɗauko Ɗabi Alonso ne ba tare da gamsuwa da shi ba.

Bayanai na cewa ko a tsohuwar ƙungiyar tasa ma, Bayer Leɓerkusen ba kowa ba ne cikin mahukuntan ƙungiyar ya amince da ɗaukarsa. To amma sai ya yi sa’ar samun haɗin kan ƴanwasan ƙungiyar.

Amma a Real Madrid duk da nasarorin da ya samu, bai samu haɗin kan ƴan wasan ba, wannan ne matsalarsa ta farko. Kowane koci na da ƙarfi da kwarjini a lokacin da ya je ƙungiya, amma ƴan wasan Madrid sun nuna masa raini tun farkon zuwansa.

Sai dai daman tun farko Ɗaɓi Alonso ya so fara aiki ne bayan Gasar Kofin Duniya ta ƙungiyoyi, ba kafinta ba sai dai Real Madrid ta nace dole sai ya fara aikin da wuri domin ya samu fahimtar juna da yan wasan ƙungiyar.

An buga gasar bayan doguwar kaka da ƴan wasan suka buga, yayin da suka gaji, wasu ke tunanin hutu, wasu kuma ke tunanin sabbin ƙungiyoyin da za su koma, bayan ƙarewar wa’adinsu.
Real Madrid dai ba ta bai wa Alonso damar tattauna hakan ba. Samun matsala da Ɓinicius Junior ne farkon abin da haifar masa cikas.

Ɗan wasan ya ɗora laifin rashin ƙoƙarinsa kan Alonso, sannan ya nuna ɓacin ransa ƙarara a cikin fili bayan sauya shi a wasan El Clasico, daga baya ya bai wa kowa haƙuri, amma ban da Alonso.

Daga nan aka jingine maganar tsawaita kwantiragin ɗan wasan don ganin abin da zai faru da Alonso. Matsalar jinya da ƴanwasan bayan ƙungiyar suka fuskanta ita ma ta kawo gagarumar matsala.

Sannan ƙungiyar ta yi watsi da buƙatarsa na ɗauko ɗan wasan tsakiyar da yake so: Martin Zubimendi, wanda daga baya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ɗauki ɗan wasan na tsakiya.
Babu haɗin kan manyan ƴanwasa don haɗe kan ƙungiyar. Ko shi Federico Ɓalɓerde ya fi damuwa da wurin da zai buga wasa maimakon haɗin kan ƙungiyar.

Shi ma Mbappe ya fi mayar da hankali kan kafa tarihi, maimakon taimaka wa ƙungiyar, inda ya ƙi yin abin da ya kamata don
warkewa daga raunin da yake da shi yanzu, don kawai kamo tarihin da Ronaldo ya kafa na cin ƙwallo 59 cikin shekara gudaƊabi bai taɓa shawo kan ƴan wasan cewa ra’ayinsa shi ne daidai ba. Kuma idan babu wannan ba zai iya yin aikinsa yadda ya kamata ba, har ya yi kamar ƙoƙarin da ya yi a Leɓerkusen.

Wane ne Arbeloa sabon kocin Madrid?

Tuni ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta naɗa Alɓaro Arbeloa, kocin ƙaramar ƙungiyar, wanda ya taɓa buga wa ƙungiyar wasanni a baya. Sabon mai horaswar ya yi shekara biyar a matsayin kocin ƙaramar ƙungiyar a Bernabeu amma bai taɓa jagorantar babbar ƙungiyar ba.

Kamar Ɗaɓi Alonso, Arbeloa ya taɓa buga wa Liɓerpool wasa kafin komawa Madrid inda ya lashe Kofin Zakarun Turai sau biyu tare da shi, sannan ya kuma taɓa cin Kofin Duniya tare da Sifaniya.

Amma masana wasanni na ganin cewa aikin da ke gabansa ba ƙarami ba ne, inda wasu ke ganin idan tsohon shahararren ɗan wasan ƙungiyar kamar Ɗabi Alonso ya kasa sauya al’adar ƙungiyar, da alama Arbeloa zai fuskanci jan aiki a gabansa.

Sannan kuma idan har ya ƙare kakar bana ba tare da kofi ba, zai yi wahala ƙungiyar ta bar shi. Amma idan ya yi sa’a ƙungiyar ta ɗauki wani kofi, to wataƙila ya tsallake siraɗi, a bashi dama domin jan ragamar ƙungiyar na lokaci mai tsawo.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *