Limaman Najeriya sun gudanar da taron addu’a kan matsalar tsaro
[ad_1]
Ƙungiyar Limaman Najeriya a wannan Alhamis ɗin ta gudanar da taron yi wa ƙasar nan addu’o’i a Jihar Kano domin neman taimakon Allah dangane da matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a faɗin ƙasar.
Taron wanda aka gudanar a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani, ya haɗa limamai, shugabannin addini da ɗimbin mabiya daga sassa daban-daban na jihar, domin roƙon Allah kan ƙalubalen tsaro da na siyasa da Najeriya ke fuskanta.
Da yake yi wa mahalarta taron jawabi, Shugaban Ƙungiyar Limaman Najeriya, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya jaddada muhimmancin tsarkake zuciya da komawa ga Allah a matsayin hanya mafi dacewa ta fuskantar matsalolin ƙasa.
Ya ce, “Mun taru a nan bisa shawarar ƙungiyarmu bayan nazarin halin da ƙasar ke ciki. Mun yanke shawarar gudanar da saukar Alƙur’ani da addu’o’i domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro.”
Sheikh Nasir ya bayyana cewa Najeriya tana fama da matsalolin ta’addanci, ’yan fashin daji da sauran barazanar tsaro, yana mai jaddada cewa addu’a ita ce babban makamin da ke hannun al’umma.
Ya ƙara da cewa, “Daga kan Boko Haram, Lakurawa, zuwa ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, duk waɗannan matsaloli ne da ba mu san da irinsu ba a baya.
“Mun fahimci cewa addu’a ita ce zaɓi na ƙarshe kuma ita ce babbar makaminmu. Haka kuma muna roƙon Allah Ya kare ƙasarmu daga duk wata barazana, ciki har da barazanar wasu ƙasashen waje da ke neman hargitsa ƙasar.”
Limamin ya kuma bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai albarka, wadda ke da yalwar albarkatun ƙasa da mutane masu juriya, inda ya yi kira ga ’yan ƙasa da su rungumi tawali’u, haɗin kai da yawan addu’a domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta tare da gina ƙasa mai cike da zaman lafiya, adalci da ci gaba.
Ƙungiyar Limaman ta buɗe ƙofar gayyata ga dukkan ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini ko aƙida ba, da su shiga wannan ƙoƙari na addu’a, ko dai a cikin ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun su.
Sheikh Nasir ya kuma yi kira ga limamai da mabiya a faɗin ƙasar da su ci gaba da yin addu’o’in neman zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa wannan taron da yanzu aka fara a Kano, za a ci gaba da gudanar da shi a dukkan jihohi 36 na Najeriya.

Masu alaƙa
[ad_2]
Source link