HOTUNA: Rayuka sun salwanta a haɗurran mota a Zariya
[ad_1]
Aƙalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon haɗurran mota uku da suka faru a wurare daban-daban a yankin Zariya, Jihar Kaduna.
Haɗurran sun auku ne a ranar Talata, 13 ga Janairu, 2026, a wasu sassa na ƙaramar hukumar Sabon Gari da ke Zariya.
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Aminiya cewa ɗaya daga cikin haɗurran ya faru ne sakamakon wata babbar motar ɗaukar lemun kwalba da ake zargin birkinta ya shanye, inda ta yi kan jama’a da ke kai-komo a hanya.
Wani mai sana’ar sayar da jarida, Malam Sani Aliyu Basasa, ya ce: “Motar ta taho da gudu bayan an yi zargin birkinta ya ƙi aiki, inda ta buge wasu kekunan adaidaita sahu da motocin da ke ɗauke da iyalai.”
Shi ma Malam Ibrahim Musa, mai sana’ar sayar da gwanjo, ya ce ɗaya daga cikin kekunan adaidaita sahun da motar ta buge ya faɗo kan kayan sana’arsa.
“Al’umma sun shiga ruɗani ganin yadda motar ta shigo cikin mutane da gudu. Ta buge kekunan adaidaita sahu, har wani yaro da ke cikin ɗaya daga ciki ya rasa ransa,” in ji shi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) a Zariya, Nasiru Abdullahi Falgore, ya ce hadurran sun faru ne a wurare uku da suka haɗa da kusa da Otel ɗin Emanto a kan hanyar Zariya–Funtua, PZ Zariya, da kuma Marabar Gwanda a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano.
A cewarsa, haɗarin farko da ya faru a Emanto ya haɗa motar Volkswagen Golf Wagon da babur, wanda ya rutsa mutane tara, mutum guda ɗaya ya rasu, mutane uku suka jikkata, yayin da aka ceto biyar ba tare da rauni ba.
Haɗari na biyu ya faru a PZ Zariya, inda motoci biyar suka yi karo da juna, ciki har da wata babbar mota, da Honda Jazz, da Peugeot 407, da kekunan adaidaita sahu biyu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa mutane goma sha biyar ne haɗarin ya rutsa da su, inda biyar suka jikkata, yayin da goma suka tsallake rijiya da baya cikin aminci.
Hukumar FRSC ta ce ta ɗauki matakan gaggawa na ceto waɗanda abin ya shafa tare da dawo da zirga-zirga a hanyoyin, tana mai kira ga direbobi da su kiyaye dokokin tuki domin kauce wa aukuwar irin waɗannan ibtila’i.




Masu alaƙa
[ad_2]
Source link