United za ta ayyana Michael Carrick a matsayin koci

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ƙulla yarjejeniya da tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick, domin ayyana shi a matsayin sabon mai horarwa na riƙon ƙwarya.

Carrick, wanda zai maye gurbin Roben Amorim, zai ja ragamar United har zuwa ƙarshen kakar wasanni ta bana.

Carrick, wanda ya buga wa United wasanni 464 cikin shekaru 12 na zamansa a ƙungiyar, ya lashe Premier 5, FA Cup 1, Carabao 3, Champions League 1, Europa 1 da kuma Club World Cup 1.

Carrick ya taɓa zama kocin United na wucin gadi lokacin da ƙungiyar ta kori Ole Gunner Solskjaer.

A yayin aikin na wucin-gadi, Carrick ya jagoranci ƙungiyar wasanni uku ciki har da wasan da ya doke Arsenal 3-2 gabanin ayyana Ralf Rangnick a matsayin sabon mai horar da ƙungiyar.

Ana tsammanin Carrick ne zai jagoranci United a wasan hamayya da za su buga a ƙarshen mako da Manchester City.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *