Waiwaye: Yadda Najeriya ta dawo mulkin Dimokuraɗiyya a 1999




Janar Abdulsalami Abubakar ya fuskanci manyan ƙalubale biyu bayan ya karɓi mulki a matsayin shugaban ƙasa a watan Yunin shekarar 1998, sakamakon mutuwar fuju’a ta Janar Sani Abacha.

Ƙalubalensa na farko shi ne yadda zai haɗa kan abokan aikinsa sojoji da ba su da matsaya ɗaya kan makomar ƙasar; Na biyu kuma, shi ne yadda zai fitar da ƙasar daga rudanin da ta shiga bayan soke zaben 12 ga Yuni, 1993 da Janar Ibrahim Babangida ya yi.

Rikicin Tsarin Mulki

Tun kafin a soke babban zaɓen shekarar 1993, Janar Babangida wanda ya yi wa Janar Muhammadu Buhari juyin mulki, ya jefa ’yan Najeriya cikin dogon tafiya da sunan shirye-shiryen komawa mulkin farar hula.

An gudanar da zaɓe ba tare da jam’iyyu ba; an kuma hana tsoffin ’yan siyasa shiga tsarin sauyin mulkin; an kafa kwamitin siyasa don ba da shawara kan tsarin mulki da tsarin muƙa mulki, daga baya aka ɗauki tsarin Option A4.

Tsarin ya yi nasarar kafa tsarin dimokuraɗiyya a matakan majalisun dokokin  jihohi da na tarayya, amma duk da haka, shirin ya ci karo da matsala a fagen zaɓen shugaban ƙasa.

A ƙarshe, Babangida ya yi murabus ya miƙa mulki ga gwamnatin riƙon kwarya ƙarƙashin jagorancin Cif Ernest Shonekan.

Sai dai Abacha ya kifar da gwamnatin riƙon ƙwaryar a ranar 17 ga Nuwamba, 1993, ya kuma kafa nasa shirin komawa mulkin farar hula wanda ya fi karkata ga burinsa na zama shugaban ƙasa, amma kuma Allah Ya yi masa rasuwa.

Lokacin Abdulsalami

Da Abdulsalami ya hau mulki, yankin Kudu maso Yamma na cikin tashin hankali saboda zargin rashin adalci a soke zaɓen 1993, kuma jama’a gaba ɗaya sun gaji da mulkin soja.

Tsohon darakta a Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Nick Dazang, ya shaida wa wakilinmu cewa a 1998 lokacin da Abdulsalami ya hau mulki, ƙasar ta fara shirin bankwana dda ogon mulkin soja zuwa ɗimokuradiyya.

Ya ce, Ansulsalami, “Ya zo ne a lokacin da ake ta ƙorafi kan soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993 da kuma abin da aka ɗauka a matsayin ƙwace nasarar zaɓen Cif Moshood Abiola da Abacha ya yi.”

Nick Dazang ya ƙara da cewa shirin Babangida da na Abacha na komawa mulkin farar hula cike yake da rikice-rikice, inda Abacha ya yi ƙoƙarin amfani da jam’iyyu biyar da suka tsaya masa don ya zama shugaban ƙasa.

Ƙungiyoyin fafutukar dimokuraɗiyya irin su CD, CLO), da NADECO sun sha gwagwarmaya. musamman NADECO, ta yi amfani da mambobinta da ke gudun hijira wajen matsa lamba ga ƙasashen waje, wanda ya sa aka tilasta wa Najeriya ta koma tsarin dimokuraɗiyya cikin gaggawa.

Mutuwar Abiola da Sabon Alkawari

Bayan wata guda da Abdulsalami ya hau mulki, Cif Abiola ya rasu.

Wannan ya haifar da tambayoyi da dama kan yadda ya mutu.

Bayan wani lokaci, hankula suka kwanta, Abdulsalami ya yi jawabi ga al’ummar ƙasa, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “damar ƙarshe da za mu daidaita al’amuranmu” sannan ya kafa kwamitin nazarin kundin tsarin mulki na 1995 tare da alƙawarin komawa mulkin farar hula.

Sabuwar INEC da Jam’iyyu

A zamanin Abacha akwai jam’iyyu biyar: UNCP, CNC, NCPN, DPN da GDM. Amma duk ba a bar su su ci gaba ba, saboda sun riga sun goyon bayan Abacha.

Abdulsalami ya rushe Hukumar zaɓe ta NECON a Agusta 1998 ya kafa sabuwar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC)ntare da naɗa Mai Shari’a Ephraim Akpata a matsayin shugaban farko.

A watan Disambar 1998, INEC ta gudanar da zaben ƙananan hukumomi a faɗin ƙasa. An kuma sanya ƙoƙarin a sakamakon zaɓen ya zama sharadi wajen rajistar sabbin jam’iyyu. Daga nan aka kafa PDP, APP da AD don su shiga zaɓen shekarar 1999.

Zaben 1999

Jam’iyyu uku suka gudanar da zaɓukan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa. AD ta yi haɗin gwiwa da APP inda suka tsayar da Olu Falae a matsayin ɗan takara, yayin da PDP ta tsayar da Olusegun Obasanjo wanda a lokacin aka sako shi daga kurkuku. APP ta ɗora Umaru Shinkafi a matsayin mataimaki ga Falae, PDP kuma ta ɗora Atiku Abubakar wanda ya lashe zaben gwamna a jiharsa.

A watan Fabrairu 1999 aka gudanar da zaɓe. APP ta samu kujeru 20 daga cikin 109 a Majalisar Dattawa da kuma 68 daga cikin kujeru a 360 a Majalisar Wakilai. A zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 29 ga Fabrairu, Obasanjo na PDP ya yi nasara da kashi 62.78% na ƙuri’un da aka kaɗa.

Falae ya ƙalubalantar sakamakon a kotu amma bai yi nasara ba.

A ranar 29 ga Mayu, 1999 aka rantsar da Obasanjo, wanda ya fara wannan tafiya ta dimokuraɗiyya da ta ci gaba har tsawon shekaru 26 – mafi tsawo tun bayan samun ’yancin kai.

Ƙalubalen Dimokuraɗiyya

Dazang ya ce: “Idan aka duba inda muka fara, INEC tana da aiki mai yawa wajen samun amincewar ’yan Najeriya. A zaɓen shugaban ƙasa na 1999, yawan masu kaɗa kuri’a ya kai 52.26%. Amma a 2023 ya sauka zuwa 26.72%. Me ya sa ’yan Najeriya da dama ke guje wa zabe? Ba INEC kaɗai ke da laifi ba. ’Yan siyasa da suka gaza wajen samar da nagartaccen mulki, suka bar ƙasar cikin tsaro mara tabbas da talauci, su ne manyan masu laifi. Amma INEC dole ta magance matsalar ƙin kaɗa ƙuri’a, ta gudanar da zaɓe mai inganci da gaskiya.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *