Gwamnatin Katsina Ta Bayyana Dalilin Sakin Mutane 70 Da Ake Zargi Da Ta’addanci


Gwamnatin Jihar Katsina ta kare matakin da ta ɗauka na amincewa da sakin mutane 70 da ake zargi da hannu a laifukan ta’addanci, inda ta bayyana hakan a matsayin dabarar ƙarfafa zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida, Dakta Nasir Mu’azu, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa, yana mai cewa sakin mutanen na daga cikin matakan gina amana da aka cimma tsakanin ƙananan hukumomin da abin ya shafa da kuma ƴan bindiga da suka tuba.

  • Gwamnatin Katsina Ta Sanya Motocin Daukar Marasa Lafiya 15 A Manyan Hanyoyi
  • Mutum Biyu Sun Rasu Yayin Rikici Tsakanin Jami’an Tsaro Da Matasa A Katsina

A cewar Mu’azu, yarjejeniyar zaman lafiyar da ta shafi aƙalla ƙananan hukumomi 15 ta haifar da sakamako mai kyau, ciki har da sakin kusan mutane 1,000 da aka sace a hare-haren ƴan bindiga a baya. Ya kwatanta matakin sakin waɗanda ake zargi da musayar fursunoni a lokacin yaƙe-yaƙe, wadda ake yi domin ƙarfafa zaman lafiya da hana sake ɓarkewar rikici.

Bayyanar ta biyo bayan martanin jama’a kan wata takardar sirri da ta bayyana cewa Ma’aikatar Shari’a ta jihar ta ɗauki matakan doka domin ganin an saki mutanen, da dama daga cikinsu na fuskantar shari’a.

Takardar, wadda Sahara Reporters ta fara wallafa wa, an rubuta ta ne a ranar 2 ga Janairu, 2026, kuma ta nemi sa hannun Kwamitin Kula da Aiwatar da Dokar Shari’ar Laifuka (ACJMC) domin sauƙaƙa sakin waɗanda ake tsare da su bisa sharuɗɗan yarjejeniyar zaman lafiya.

Kwamishinan ya ƙara da cewa yarjejeniyar ta haifar da sakin mutane a ƙananan hukumomi da dama kamar Sabuwa, da Bakori, da. Danmusa, da Dutsinma, da Kurfi, da Safana, da Malumfashi da kuma Jibia, inda wasu wurare suka samu sakin ɗaruruwan mutane.

Ya jaddada cewa wannan mataki bai saɓa wa doka ba, yana mai cewa duk wanda bai gamsu da matakin ba na da ƴancin bin hanyoyin shari’a. Duk da haka, lamarin na ci gaba da jawo muhawara, inda wasu ke ganin hakan na iya raunana adalci, yayin da wasu ke cewa zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar tattaunawa da sassauci.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *