Wang Yi Ya Gabatar Da Shawarwarin Kara Zurfafa Kawancen Sin Da Afirka
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan harkokin waje da hadin gwiwa da sassan gabashin Afirka na kasar Tanzania Mahmoud Thabit Kombo, jiya Jumma’a a birnin Dar es Salaam, inda ya yi kira da a kara zurfafa kawancen Sin da kasashen Afirka.
Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce ziyararsa ta bana, ci gaban dadaddiyar al’ada ce da ministocin harkokin wajen kasar Sin suke aiwatarwa, ta sanya kasashen Afirka zangon farko a kasashen ketare da suke ziyarta duk shekara cikin shekaru 36 a jere, kuma al’adar da Sin za ta ci gaba da nacewa da kuma wanzar da ita.
Ya ce hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, muhimmin bangare ne cikin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, mai cike da karsashi da makomar ci gaba mai haske.
Ministan harkokin wajen na Sin, ya kuma takaice sassan kawancen Sin da Afirka, da amincewa juna tsakaninsu cikin manyan fannoni uku. Na farko hada karfi wajen kare adalci. Na biyu kuma hada kai wajen neman ci gaba. Kana na uku rajin cimma moriyar bai daya.
Wang, ya ce Sin a shirye take ta kara daidaita dabaru tare da kasashen Afirka, da ingiza sauri, da fadada aiwatar da sakamakon dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC wanda ya gabata a birnin Beijing, dangane da hadin gwiwar Sin da Afirka, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar bai daya a sassa irin su noma, da hakar ma’adinai, da raya masana’antu, da bunkasa tafiya kafada-da-kafada a turbar zamanantar da sassan biyu. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link