Mun miƙa wa Fubara takarda shirinmu na tsige shi — Majalisar Ribas

[ad_1]



Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta ce tana kan bakanta na shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu ba, kuma an riga an miƙa musu takardun sanarwa kan zarge-zargen da ake yi musu.

Majalisar, karkashin jagorancin Kakakinta, Martin Amaewhule, ta fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa ne a ranar Alhamis, bisa wasu tuhume-tuhume guda takwas.

Sai dai a ranar Juma’a jita-jita suka bazu a shafukan sada zumunta cewa Majalisar ta sake janye sanarwar tsige gwamnan da mataimakin gwamnan.

Amma Shugaban Kwamitin Watsa Labarai, Koke-koke da Korafe-korafe na Majalisar, Dakta Enemi Alabo George, ya sanar da yammacin Juma’a cewa ana ci gaba da shirin tsige su, yana mai bayanin cewa kundin tsarin mulki ya bai wa Majalisar ikon daƙile duk wani take haƙƙin kundin tsarin mulki da gwamna, mataimakin gwamna ko wani jami’in gwamnatin Jihar Ribas zai yi.

Ya ce: “Majalisar Dokokin Ribas na farin cikin sanar da al’ummar jihar cewa shirin tsige da Majalisar ta fara a ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026, yana tafiya yadda ya dace bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.

“An mika takardun zarge-zargen manyan laifuka da aka gabatar bisa Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulki ga Gwamna da Mataimakiyarsa ta hannun Shugaban Majalisar, yayin da muke jiran amsoshinsu.

“Kamar yadda kowa ya sani, Kundin Tsarin Mulki ne ya bai wa Majalisar Dokoki ikon tsayawa tare da al’umma domin daƙile duk wani take hakkin kundin tsarin mulki da gwamna, mataimakin gwamna ko wani jami’in gwamnatin Jihar Rivers zai aikata, don haka muna kan wannan nauyi yadda ya kamata.

“Mun lura cewa wasu mutane da kafafen yada labarai na kokarin yaudarar jama’a, musamman ta hanyar yaɗa jita-jitar cewa an dakatar ko an soke shirin. Wasu na ƙirƙirar labaran ƙarya ne domin haddasa rashin jituwa tsakanin Majalisar da ’yan Najeriya masu kishin ƙasa.

“Saboda haka, da izinin shugaban Majalisar, Rt. Hon. Martin Chike Amaewhule, ina kira ga kowa da kowa da ya yi watsi da waɗannan dabaru, domin tuni sun ci tura.

“Muna nan daram kan ayyukanmu na kundin tsarin mulki, kuma ba za mu bari barazana ko cin mutunci daga waɗanda ba su yi wa dimokuradiyyarmu fatan alheri ba su karkatar da mu.

“Muna godiya ga al’ummar Jihar Ribas bisa addu’o’i da ƙwarin gwiwar da suke ba mu, tare da miƙa godiyarmu ga dukkan masu ruwa da tsaki da shugabanni a dukkan matakai. Haka kuma, muna amfani da wannan dama wajen jinjina wa dukkan masu kishin dimokuraɗiyya da ke da yakini ga gina Najeriya,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *