Manufar Yada-Zango Ba Tare Da Bukatar Biza Ba Ta Bunkasa Adadin Masu Shigowa Kasar Sin Domin Ziyara
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron al’umma ta kasar Sin Zhang Ming, ya ce adadin mutanen da suka shigo don ziyartar kasar Sin a shekara, tun bayan kaddamar da manufar nan ta yada-zango na tsawon sa’o’i 240 ba tare da bukatar neman biza ba, ya kai mutum miliyan 40.6, adadin da ya karu da kaso 27.2 a mizanin shekara.
Zhang Ming, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, ya kara da cewa adadin matafiya bayan kaddamar da kwaskwarima ga manufar ya karu da kaso 60.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara, idan an kwatanta da matakan da kasar ke aiwatarwa gabanin kaddamar da manufar.
An kaddamar da manufar yada-zango a kasar Sin ba tare da bukatar biza ba a karon farko a watan Disamban shekarar 2024, kuma ya zuwa yanzu, an fadada yawan kasashen da al’ummunsu ke da damar cin gajiyarta zuwa 55. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link