Mangal ya yi wa mutum 18,000 aikin ido kyauta a Katsina




Hamshaƙin ɗan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, ya ɗauki nauyin tallafa wa masu ƙaramin karfe 18,000 da aikin ido kyauta daga ciki da wajen jihar Katsina.

Wannan dai wani ɓangare ne na mutanen da ɗan kasuwar ke tallafawa masu fama da cututtuka daban-daban a kowace shekara.

Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin amintattu da ke kula da aiwatar da shirin, Malam Hussaini Kabir, ya ce aikin tiyatar idon da ake gudanarwa a Asibitin Ido na cikin garin Katsina shi ne zangon ƙarshe na shekarar 2025.

“Manufar wannan shirin tallafin kiwon lafiya ga marasa ƙarfi ita ce rage wa gwamnati nauyin kashe kuɗin kula da lafiya, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi da ke fama da matsalolin rayuwa,” in ji shi.

Daga cikin waɗanda suka amfana akwai Malam Usman, wanda ya ce: “Rabon da in ga wani abu da idanuna an fi shekara biyu, amma yau ga shi ina ganin komai. Kai ma da ke tsaye gaba na ina ganinka da fararen kaya da hular dara ja.”

Haka kuma Malama A’isha daga Bakori ta bayyana farin cikinta da cewa: “Na dade ina neman magani amma ba a dace ba. Amma zuwana nan Allah Ya sa an dace. Na ji ana sanarwa ga masu lalurar ido, shi ne na zo. Yanzu kwana na uku kenan, abinci ma ana kawo mana har mu bar wa almajirai.”

Alhaji Ɗahiru Mangal dai ya shahara a jihar Katsina wajen tallafawa marasa ƙarfi ta fannoni da dama, musamman abin da ya shafi ciyarwa da kuma ɗaukar nauyin kula da lafiya.

Tallafinsa ya haɗa da marasa lafiya masu fama da larurar mafitsara, cutar gwaiwa, ciwon ido da makamantansu.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *