IAR ta ƙirƙiro sabon taki mai rahusa ga manoma

[ad_1]



Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (IAR) ta gabatar da sabbin nau’ukan takin zamanin da ta ƙirƙiro masu rahusa.

Cibiyar dai ta ƙirƙiri takin ne samfuran Nutracoat da Nutramix, tare da haɗin gwiwar kamfanin Universal Speciality Chemicals, waɗanda za su taimaka wa manoma rage kuɗin da suke kashewa wajen noma da kashi 30 zuwa 40 cikin 100.

Da yake bayani kan sabbin takin, Shugaban Sashen Malaman Gona na cibiyar, Dokta Sharhabil Yahaya Musa, ya ce takin yana da inganci wajen samar da amfanin gona mai yawa da kuma ingantacciyar yabanya.

Ya ce an samar da wannan samfurin ne domin sauƙaƙa wa manoma ci gaba da noma, musamman a lokacin da darajar amfanin gona ke ƙasa kuma farashin taki ke ƙaruwa.

Ya ƙara da cewa babu abin da zai sa manoma su ji tsoro game da wannan sabuwar fasaha da cibiyar ta samar.

Dokta Sharhabil ya yi kira ga kamfanin da ya sauƙaƙa wa manoma hanyar samun takin cikin sauƙi idan suka tashi saye.

A cewarsa, idan manoma suka sami taki cikin sauƙi, hakan zai ƙara yawan abin da suke nomawa da kashi 30 zuwa 40, wanda ke nuni da ribar da za su samu.

Ya shawarci manoma da su yi amfani da takin a noman rani da damina a dukkan nau’o’in amfanin gona da suke nomawa.

A nasa jawabin, Bengum Hyelatakiri na kamfanin taki ya bayyana cewa Nutracoat NPK da Nutramix UREA za su rage kuɗin taki da kashi 30 zuwa 50 ga manoma.

Ya kuma tabbatar da cewa takin ba ya cutar da ɗan adam ko ƙasar noma, domin an yi shi ne daga tsirrai.

Bengum ya tabbatar wa manoma cewa kamfanin zai samar da takin ba tare da wahala ko tsadar da za su fuskanta ba.

Wasu daga cikin manoman da suka yi amfani da takin a gonar gwaji sun bayyana gamsuwarsu bisa yadda suka ga ingancin takin da kuma yawan amfanin da suka samu.

Manoman sun roƙi kamfanin da ya samar da takin a wuraren da suke, domin sauƙaƙa musu wajen saye.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *