Da Ɗumi-ɗumi: Kotu Ta Bayar Da Belin Malami, Matarsa Da Ɗansa Kan N1.5bn

[ad_1]

Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da belin tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da matarsa da ɗansa a kan kuɗin Naira miliyan 500 kowannensu.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ce kowannensu zai kawo mutane biyu da za su tsaya masa.

  • Amurka Za Ta Rasa Matsayinta Na Jagorancin Duniya – Mahdi Shehu
  • Za Mu Baza Ƙarin Jami’anmu A Faɗin Nijeriya Don Samar Da Tsaro – Sojoji

Mutanen dole ne su kasance sun mallaki ƙas a Asokoro, Maitama, ko Gwarinpa a Abuja.

Ma’aikacin kotun mai kula da rajista zai tabbatar da takardun ƙasar waɗanda za su tsaya musu.

Haka kuma, dole ne waɗanda za su tsaya musu su kasance masu kuɗi don iya karɓar belinsu.

Alƙalin ya kuma umarci Malami da iyalinsa su miƙa fasfo ɗinsu ga kotu.

Ba za su iya fita ƙasashen waje ba sai da izinin kotu.

Ana tuhumar Malami, matarsa da ɗansa da laifukan cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da muƙamansu ba daidai ba lokacin da Malami yake Ministan Shari’a.

Kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a wani lokaci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *