Dalilin Da Ya Sanya Gwamnatin Gombe Ta Haramta Sana’ar Bola Jari
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da dakatar da sana’ar Bola jari da aka fi sani da gwangwan inda ta yi nuni da karuwar barazanar tsaro da kuma barnata kayayyakin more rayuwa na jama’a.
An yanke wannan shawarar ne a ranar Litinin bayan wani taron Majalisar Tsaron Jihar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.
- Yawan Fasinjojin Jiragen Sama A Sin Ya Kai Matsayin Koli A Duniya
- An Tsara Kasafin Kuɗin 2026 Don Ƙarfafa Nasarorin Da Shirye-shiryen Tinubu Ke Samu — Minista
A lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Zubair Umar, ya ce majalisar ta lura cewa masu sana’ar ba su da “tsarin shugabanci da aka amince da shi ballantana kuma ingantaccen tsarin dokoki,” wanda hakan ya sa, ba za a iya lura da ayyukansu ba.
Don haka, “majalisar, nan take ta haramta duk wani nau’in sana’ar gwangwan a fadin jihar,” in ji Umar.
Ya bayyana cewa rahotannin leken asiri da tsaro da aka gabatar wa majalisar sun nuna cewa, ana lalata kayayyakin gwamnati, musamman makarantu, kuma ana sayar da kayayyakin ga dillalan sana’ar ta karafa.
“Wannan haramcin zai ci gaba da aiki har sai dillalan sun tsara kansu yadda ya kamata a karkashin jagorancin da aka amince da shi, bayan haka, shi ne gwamnati za ta kafa cibiyar da za ta lura da sana’ar a karkashin kulawar tsaro,” in ji Umar.
[ad_2]
Source link