Bai kamata a zargi Abba da cin amana ba — Shekarau

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce bai dace a zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da cin amana ba dangane da jita-jitar cewa zai fice daga jam’iyyar NNPP.

Malam Shekarau ya bayyana cewa sauya sheƙa a siyasa ra’ayi ne wanda ya dogara da shawara da kuma halin da aka tsinci kai a ciki.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da kafar DCL Hausa, inda ya soki kalaman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya ce ya kamata Gwamna Abba ya ajiye kujerarsa idan ya fice daga NNPP.

A cewarsa, wannan magana ba ta dace ba, domin shi kansa Kwankwaso ya taɓa barin jam’iyya da lokacin da yake kujerar gwamna, inda ya koma APC daga PDP ba tare da ajiye kujerar ba.

Shekarau ya ce irin abin da Kwankwaso ya yi a baya shi ne ake ganin Gwamna Abba zai iya yi yanzu, don haka bai kamata a ɗauki hakan a matsayin cin amana ba.

“Ya kamata a ƙyale Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar da ya ga ta dace ba tare da an riƙa yi masa kallon maci amana ba.

“Kwankwaso kansa ya sauya sheƙa sau da dama — daga PDP zuwa APC, ya dawo PDP, sannan daga bisani ya koma NNPP.

Har ila yau, Shekarau ya tuno da yadda aka kafa jam’iyyar NNPP a Kano, inda ya ce saɓani kan rabon muƙamai ne ya sa shi da magoya bayansa suka fice daga jam’iyyar.

Ya bayyana cewa an kafa kwamiti domin tsara rabon muƙamai, inda aka naɗa Gwamna Abba shugaban kwamitin, amma bayan watanni babu wani sakamako mai gamsarwa, lamarin da ya janyo rashin jituwa.

A ƙarshe, Shekarau ya jaddada cewa duk wani ɗan siyasa na da ‘yancin yanke shawara bisa la’akari da ra’ayin magoya bayansa, kuma bai kamata a riƙa ɗaukar sauya sheƙa a matsayin cin amana kai tsaye ba, musamman idan akwai dalilai masu ƙarfi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *