Kwana 25 ke nan ban ji muryarsa ba — Matar Sheikh Khalifa Sani Zaria
Matar malamin addinin Musulunci da ake tsare da shi, Hajiya Ramatu Khalifa Sani Abdulƙadir Zaria, ta ce yanzu kwanaki 25 ke nan ba ta sake jin muryarsa ba tun bayan tafiyarsa zuwa Abuja.
Hajiya Ramatu, a wata hira da ta yi da RFI Hausa, ta ce, “Ni dai da asubahi ya fito ya ƙwanƙwasa min ƙofa ya ce har yanzu ban tashi daga barci ba, na ce masa na tashi ina addu’a ne. Sai ya ba ni kuɗin cefane ya ce min zai je Abuja idan Allah Ya yarda zai dawo a ranar.
“Sai na ce masa Allah Ya tsare hanya. Tun daga ranar har yanzu ban ƙara jin muryarsa ba, idan na kira layinsa a kashe. Yau kwanaki 25 ke nan ban sake jin muryarsa ba.”
Ta ƙara da cewa tun bayan ɓacewar mijinta take zaune ita kaɗai a gida tare da yara, lamarin da ya jefa ta cikin tashin hankali da damuwa.
“Ni kaɗai a gida sai yara. Tashin hankali kam ina ciki. Idan ina zaune, sai in rika jin jiri, ba na iya barci. Tashin hankali kam kowa ya san kana ciki, to amma nakan daure saboda yara kada hankalinsu ya tashi.”
Hajiya Ramatu ta ce duk da halin damuwar da suke ciki, suna bin irin nasihohin da malamin ya taɓa yi musu.
“Da yake ya tarbiyantar da mu a kan mu riƙa yin haƙuri da miƙa lamarinmu ga Allah, shi ne muke koyi da shi. Amma muna cikin damuwa.”
Ta kuma bayyana abin da ta sani game da tafiyar mijinta zuwa Abuja, inda ta ce, “An ce wai an kulle asusu ɗinsa kuma wai sai ya tafi Abuja ne za a iya buɗewa. Daga zuwa sai aka ce wai ana tuhumar sa a kan wasu Naira miliyan biyu. Haka dai aka faɗa min tunda ni ban je ba.”
A nasa ɓangaren, ɗan malamin mai suna Sunusi Khalifa Sani Abdulƙadir, ya bayyana cewa bayan an rufe asusu ɗin mahaifinsa ne aka nemi su tafi Abuja.
“Bayan an rufe asusu ɗinsa sai ya nemi jin dalili, aka ce wai EFCC ne suka rufe kuma sai an koma wajensu ne za a iya buɗewa.
“Shi ne muka tafi Abuja tare da shi zuwa ofishin EFCC. Bayan an yi wa Sheikh tambayoyi sai suka ce wai akwai miliyan biyu da aka turo masa, shi ake magana a kai.”
Sunusi ya ce mahaifinsa ya bayyana wa jami’an EFCC cewa akwai wanda ya haɗa shi da wani mutum domin a yi masa addu’a kan harkokinsa na rayuwa, kuma ya aiwatar da abin da aka nema a gare shi.
Ya ƙara da cewa daga nan aka shaida musu cewa batun ya shafi sojoji.
“Daga nan sai suka ce dama kes ɗin sojoji ne, don haka sai suka sanar da sojoji cewa sun masa tambayoyi kuma Sheihi ya amince zai mayar da kuɗin. Sai sojoji suka ce za su zo domin yi wa Sheihi tambayoyi. Tun daga wannan rana yau kwanaki 25 ke nan ba mu gan shi ba.”
Ya kuma bayyana cewa a cikin kwanaki 25 ɗin an ba mahaifinsa wata lamba ya kira shi ya ce yana nan lafiya, amma har yanzu ba su san dalilin ci gaba da tsare shi ba, kuma ba su san inda yake ba ko halin da yake ciki.
Da aka tambaye shi game da zargin cewa an kama malamin ne saboda wai yana yi wa masu yunkurin yin juyin mulki addu’a, Sunusi ya ce ba su da masaniya a kan hakan.
“Ba su bayyana mana hakan ba, kuma har yanzu hukumomi ba su ce mana hakan ba.”
Game da ko wanda ya ba wa Sheihi kuɗin soja ne, Sunusi ya ce ta waya aka yi hulɗar, kuma almajirin malamin ne ya haɗa shi da mutumin. Ya ce mahaifinsa manomi ne tare da koyar da addini da yi wa mutane masu neman biyan buƙata addu’a.
A ƙarshe, Sunusi ya yi kira ga hukumomi da su sake mahaifinsu.
“Ni fatan a sake mana mahaifinmu domin tun daga lokacin da abin ya faru ba na barci. Duk sanda muka farka cikin dare da mun tuna abin sai kuka.”