Ana fargabar kashe sojoji 2 a rikicin manoma da makiyaya a Taraba




Wasu rahotanni da ba a kai ga tantancewa ba ana fargabar akwai sojoji biyu a cikin mutanen da aka kashe a rikicin manoma da makiyaya a karamar hukumar Karim Lamidon jihar Taraba.

An gano cewa rikicin ya barke ne da safiyar Laraba tsakanin al’ummar Bandawa da makiyaya.

Sojojin, wadanda ke runduna ta shida ta sojojin kasan Najeriya da ke Jalingo dai an girke su ne a yankin mai fama da rikici, lokacin da lamarin ra ritsa da su.

Kazamin rikici tsakanin al’ummomin manoma na Bandawa da Munga Doso da kuma Fulani makiyaya kimanin wata biyu da suka gabata dai ya yi sanadin rasa rana sama da mutum 50 tare da rasa dukiya ta miliyoyin Naira.

Kazalika, rikicin ya kuma raba iyalai da dama a yankin da muhallansu.

Arangamar ta baya-bayan nan na zuwa ne bayan tattaunawar zaman lafiya daban-daban da aka yi a a garuruwan Lau, Jalingo da Karim Lamido, amma har yanzu ba a ga wani ci gab ana ku zo ku gani ba.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin mai rikon mukamin Kakakin Rundunar Sojojin Kasa, Laftanar Umar Mohammed, don yin tsokaci a kan rikicin ya ci tura saboda layinsa ya kasance a rufe.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *