Wike Ya Gargaɗi Sakataren APC Na Ƙasa Da Ya Nisanci Siyasar Ribas
[ad_1]
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya gargaɗi Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, da ya daina tsoma baki a siyasar Jihar Ribas, yana mai buƙatar ya riƙa taka-tsantsan da kalaman da yake furtawa. Wike ya yi wannan gargaɗi ne yayin ziyarar “godiya” da ya kai Karamar Hukumar Oyigbo a Jihar Ribas.
Wike ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar APC ta karɓi wasu kuɗaɗe daga cikin naira biliyan 600 da ke asusun gwamnatin Jihar Ribas, yana mai cewa jihar “wuri ne da ba a yarda a tsoma baki ba.” Wannan na zuwa ne bayan da Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Kudu, Victor Giadom, ya bayyana Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin “jagoranta,” furuci da ya jawo cece-kuce a siyasar jihar.
- Ba Zan Goyi Bayan Tinubu A 2027 Kamar Wike Ba — Makinde
- Canada Za Ta Caka Wa Kanta Wuka Kan Matakin Da Ta Dauka A Kan Kasar Sin
Sai dai Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya soki kalaman Giadom, yana mai cewa muƙamin gwamna matsayi ne mai daraja da ya kamata a girmama duk wanda ke riƙe da shi, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba. Basiru ya bayyana hakan ne a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Lahadi, yana mai cewa kalaman cin mutunci ne ga gwamna ba su dace ba.
Da yake mayar da martani, Wike ya ƙalubalanci Basiru, yana mai gargaɗin cewa duk wanda ya tsoma baki a harkokin Jihar Ribas zai fuskanci sakamako. Ya ce bai kamata a ɗauki goyon bayan da al’ummar Ribas ke bai wa Shugaba Bola Tinubu a wasa ba, yana mai jaddada cewa “duk abin da ya faru, wanda ya tsoma baki shi ya jawo wa kansa,” tare da bayyana Ribas a matsayin jihar da ba a yarda da tsoma baki daga waje ba.
[ad_2]
Source link