Asalin Abin Da Ya Faru Da Sheikh Sani Khalifa, Daga Bakin Ɗansa
[ad_1]
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Kalifa Zaria, bayan kwashe kwanaki fiye da 21, har yanzu iyalansa basu san inda yake ba.
A yayin tattaunawa da manema labarai, ɗaya daga cikin ‘ya’yansa mai suna Muhammadu Nafsu Zakiyya Sani Kalifa Zaria, ya bayyana yadda lamarin ya faru da cewa:
- Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi
- A Bangaren Kyawawan Dabi’u, Annabi SAW Ma’aiki Ne Ga Duk Halitta
Akwai wani muridin (mabiyi) Sheikh Sani Kalifa wanda kuma Jami’in soja ne, ya zo wurin Sheikh da wata buƙata ta neman addu’a daga maigidansa a wurin aiki (babban jami’in soja), kan wani al’amari da suke shirin aiwatarwa Allah ya basu sa’a.
Nan take, sai wannan muridi ya kira ogansa a waya, ya haɗa shi da Sheikh Kalifa don su gaisa, sai wannan oga, babban jami’in soji, ya ce, “Malam ka taya mu da addu’a, akwai wani babban aiki da muke shirin aiwatarwa, Allah ya bamu sa’a.” Ba tare da ya bayyana wa Sheikh Kalifa irin abun da suke shirin aiwatarwa ba. Daga nan, sai ya nemi Kalifa ya tura asusun Banki domin sanya abun sadaƙa.
Bayan sun gama waya, sai wannan muridi ya karɓi nambar asusun Sheikh ya tura wa Ogansa, aka tura Naira miliyan biyu (N2,000,000) acikin asusun. Bayan kwana biyu, Sheikh Kalifa ya tura a ciro kuɗi a asusun, sai aka ce masa, an rufe asusun.
Da zuwan Sheikh Kalifa Bankin domin a gyara matsalar, sai aka sanar da shi cewa, matsalar daga EFCC ce kuma dole sai an je ofishinta da ke Abuja.
A wata ranar Alhamis, bayan sallar Asuba, Sheikh Kalifa suka shiga mota zuwa ofishin EFCC da ke Abuja, da isarsu, jami’an hukumar suka yi musu bayani cewa, wannan miliyan biyu da aka tura, itace sanadi, sai ya yi musu bayanin yadda kuɗin suka samu, sai suka ce to ya ɗan jira. Yana nan zaune, sai ga jami’an sojoji sun shigo, sai suka ce suna son za su yi wa Sheikh Kalifa bincike amma ba a nan za a yi ba, kuma binciken ba zai wuce sa’o’i uku kacal ba. Jami’an sojin, sun tafi da wani daga cikin ‘ya’yansa mai suna Ibrahim amma sun sauke shi a hanya.
A yayin wannan tattaunawar, an haura sati uku ba muga Sheikh Kalifa ba, sai dai ranar da ya cika sati ɗaya a wurinsu, sun bashi waya ya tuntuɓi iyalinsa. Yanzu ya zama sati biyu kenan ba a sake jin muryarsa ba.
Da aka fara bincike, sai aka gano cewa, wannan asusun da aka turawa Sheikh Kalifa kudi, ana zargin asusun wani babban jami’in soja ne da ake zargin yana daga cikin jami’an sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watannin baya.
Nafsu Zakiyya, ya tabbatar da cewa, duk sun bi shugabannin Siyasa da ke Zaria, musamman kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da sarkin Zazzau, Alhaji Nuhu Bamalli domin ganin an san halin da Sheikh Kalifa ke ciki, kuma mun tabbatar dukansu suna iya bakin ƙoƙarinsu. Amma komai, za a gaya mana, in ba mun ganshi ba, hankali ba zai kwanta ba, musamman duba da shekarunsa sama da 75, riga ɗaya, takalmi ɗaya, da hula ɗaya da ya tafi da su.
[ad_2]
Source link