Sauya Sheka: Gwamna Abba Ya Yi Daidai

[ad_1]

Daga Muktar Anwar

Batun sauya sheka daga wannan jam’iyyar siyasa zuwa waccan, wani alamari ne da yake da dogon tarihi a siyasar wannan kasa, faro tun daga jamhuriyar siyasa ta farko a Nijeriya. Gwari-gwari, tun kafin wannan asa ta Nijeriya ta kai ga samun ‘yancin-kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya, canjin jam’iyya ya zama-jiki.

Manyan shehunai kuma hafizan siyasa na-dauri a kasa, tarihin rayuwar siyasarsu ba shi kammaluwa, dole sai an sirka da tsallakawa daga wannan jam’iyyar siyasa zuwa waccan. Ba kowa ne ya sani cewa, su marigayi Malam Aminu Kano da Malam Sa’adu Zungur da ire-irensu, jam’iyyar NPC ce suka fara yi farko, kafin su tattara kayansu zuwa jam’iyyar NEPU. Yaushe ne a siyasar Nijeriya sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan ya zama zunubi, ko a ce ya zamto riddar siyasa?.

Wancan tarihi na sauya sheka da ya faro asali tun daga jamhuriyar farko ta siyasa a Nijeriya, wanda su Malam Aminu Kano suka sunnanta, ya ci gaba da mirginawa ne har zuwa jamhuriyar siyasa ta biyu, wadda ta fara daga Shekarar 1979, Shekaru 3 bayan kashe Janar Murtala Ramat Muhammad. Wadanda za a iya sanya su a rukuni na biyu cikin sawun dattijan siyasar Arewacin wannan kasa, mutane irin su marigayi Alhaji Abubakar Rimi, da marigayi Alhaji Balarabe Musa, da sauransu, sune kan gaba wajen ci gaba da dabbaka sunnar canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan, kamar yadda magabatansu, kuma iyayensu a siyasa (su Malam Aminu Kano) suka yi. Su Rimin, sun yi kaura daga jam’iyyar PRP zuwa jam’iyyar NPP, a Shekarar 1981. Saboda haka, yaushe ne sauya shekar ya zama munafunci, ko haramun, koko ridda a siyasar Nijeriya?. Wannan dalili, na daga hujjojin da masu ra’ayin gwamna Abba na da cikakken “yancin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC suka dogara da.

A kullum, tarihi dai shi ke takan maimaita kansa a kowane irin janibi kuwa na rayuwar yau da kullum. Wannan kuma amsa ce ga masu cewa, don me yasa Abba Gida Gida zai bar wanda ya dauko shi a lokacin da shi ba kowa ne ba a fagen siyasar Kano, ya tallata shi, kuma aka zabe shi don shi, amma saboda butulci ya fice daga jam’iyyar wannan maigida nasa na siyasa zuwa wata, ba tare da jiran maigidan ya jagorance su zuwa sabuwar jam’iyyar ba?. A nan, masu irin wannan tambaya na nufin, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya yi cikakken gatan siyasa ga Abba Gida Gida, ta hanyar zakulo shi a tsakanin wadanda suka fi shi cancanta a siyasar Kano, yai masa riga da wando na siyasa, kuma ya maishe shi gwamnan Kano. Babu shakka, jama’ar Kano sun zabi Abba ne saboda Kwankwaso!. Kamanceceniyar hakan a siyasar Kano shi ne, a jamhuriyar siyasa ta biyu a Kanon, marigayi Engr. Salihi Iliyasu ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PRP, wanda daga bisani hukuma ta ayyana shi a matsayin wanda bai cancanci tsayawa wannan takara ba, bisa kafa hujjar rashin biyan haraji.

Bayan hukuma ta kassara takarar Salihi Iliyasu, babu wani mahaluki da ke tare da Malam Aminu Kano a wancan lokaci, wanda zai yi tunanin cewa, Aminu Kano zai mayegurbin takarar Iliyasu da Muhammadu Abubakar Rimi, kasantuwar da yawa akwai wadanda suka fi shi cancanta da wannan takara gewaye da Malam. Amma haka aka dauko Rimi, wanda a lokacin, ko takarar Sanata babu wanda zai yi tunanin ya cancanta ya nema, aka ba shi takarar gwamnan Kano, kuma ya lashe zaben. Duk saninka da tarihi, ko iya sharhin siyasa, babu wata hujja da take gare ka, wadda za ta gamsar da Duniya cewa, an zabi Rimi ne saboda cancantarsa, ko don shahararsa a fagen siyasa. Tilas dole a yarda cewa, jama’ar Kano a wancan lokaci, sun zabi Rimi ne saboda Aminu Kano, tamkar irin yadda jama’ar Kano suka zabi Abba, saboda Kwankwaso.

Duk da an zabi Rimi gwamna saboda Malam, bai sa yayinda Rimi zai tsallaka titi, ya jira Aminu Kano ya rike masa hannu sun tsallaka tare ba. Ma’ana, Rimi bai jira lamuncewar maigidansa kuma babansa na siyasa Aminu Kano ya ba shi izini, ko a ce sun canja jam’iyyar siyasa tare ba, daga PRP zuwa NPP. Wannan ke nuna halasci a tarihance, na, Abba Gida Gida na iya tsalle daga NNPP tare da direwa cikin jam’iyyar APC, ba tare da wajabta masa cewa, dole ne sai sun koma tare da Kwankwaso maigidansa ba. Hakika, da mutane na yin izina da tarihi, da wasu kace-nace ba su faru a tsakani ba.

Butulcin Abba Ga Kwankwaso

Duk da halasci da Abba ke da shi a siyasance na canja jam’iyyar siyasa da ta maigidansa, wanda tarihin siyasar Kano da ma na Kasa suka halasta yin haka, har yanzu akwai wadanda ke yi masa kallon butulu ga maigidansa Kwankwaso. A wajensu, tun da Kwankwaso ne silar Abba ya zama gwamnan Kano, lallai ne ya ci gaba da zama tare da shi a siyasance, su mutu tare, su kife tare, kuma a binne su kabari daya tare a siyasa.

Da yawan masu sharhin siyasa a garin Kano da ma matakin kasa, na masu cewa, babu wani mutum a tarihin siyasar Kano, wanda ya raba-gari tare da rabuwa dutse a hannun riga da masu gidansa na siyasa tamkar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Sun kara da cewa, tarihin siyasar Kwankwaso da gawurtarsa, ba zai cika ba, sai da tulin wasu abubuwa da za a iya fassara su da tsantsar yin butulci ga iyayensa da kakanninsa na siyasa. Masu sukar Abba da butulcin siyasa ga Kwankwaso, da za su bibiyi tarihin siyasar Kwankwaso ciki-da-bai, da mai yi wa, sai dai a fassara Kwankwason ma da cewa, shi ne ya kawo butulcin siyasa Duniya, musamman a jihar Kano.

Sanata Hamisu Musa Kafin Agur

Wadanda suka san marigayi Sanata Hamisu Musa Kafin Agur, wanda suke cikin karamar hukuma guda da Sanata Kwankwaso, kowa ya san shi ne ya rike hannu Kwankwaso, ya tsoma shi cikin lamuran siyasa a Kano, ya hada shi da manyan jagororin gidajen akidun siyasa na Kanon. Amma a karshe, sun raba garin siyasa da shi ne cikin mummunan yanayi.

Aminu Wali Da Musa Gwadabe

A wannan jamhuriyar siyasa ta hudu da muke, wadda a cikinta ne aka fara jin amon Kwankwaso, har ya yi suna, ya gawurta, ya yi dacen samun ruhin da yawa daga matasa tamkar irin yadda marigayi Marwa Maitatsine ya yi katarin samu, bai kai ga samun wannan shuhura ta siyasa ba, sai da taimakon mutane irin su marigayi Malam Musa Gwadabe da kuma Alhaji Aminu Wali. Sai dai a karshen lamari, an rabu ne, rabuwa ta uwaka-ubaka, tsakanin Kwankwason da wadannan dattijan mutane a siyasar Kano da ma ta Nijeriya bakidaya.

Ta tabbata cewa, lokacin da aka yi zaben cikin gida na gwamna a Kano, cikin Shekarar 1998, Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben ba Kwankwaso ba, amma daga bisani mene ne ya faru?. Duk da Kwankwaso ya sha kashi a zaben, dole aka zo aka hakurkurtar da maigidan Ganduje Rimi, aka riginginta aka barwa Kwankwaso takarar, duk da ba shi ne ya ci ba. Su waye suka jajirce sai an bai wa Kwankwaso takarar gwamnan?. Su Wali ne da Gwadabe! Amma a karshe, yaya alakarsu da Kwankwaso ta kare a siyasance?.

Bayan Obasanjo ya bai wa Musa Gwadabe minista, Kwankwaso ne ya matsa lamba, dole sai da Obasanjo ya cire dattijo Musa Gwadabe daga wannan kujera ta minista. Duk iya sharrin mutum da kwakule kwakulen laifin mutane, ba shi da hujjojin da zai zo Kano, ya zaiyano rashin kirkin marigayi Malam Musa Gwadabe a siyasance, wanda ake yi wa lakabi da “Damo Sarkin hakuri”.

Shi kuwa Aminu Wali, bayan Kwankwason ya watsar da shi a siyasance, akwai lokacin da yaran Kwankwason suka yi garkuwa da shi a kofar gidan marigayi Sarkin Kano Ado (garkuwa irin ta siyasar Kano), suka tube masa hula, aka rika dungure masa kai, duk da ya haura Shekaru 80 a Duniya a wancan lokaci. Babban zunubinsa shi ne, ya rabu da Kwankwaso a siyasa!!!.

Muhammadu Abubakar Rimi

Mutumin yake a Kano, ko yake bibiyar siyasar Kano, ya kwana da sanin irin yadda Kwankwaso ya rika bi yana take duk wani motsin siyasar marigayi Abubakar Rimi. A fili yake Rimin nan, ya fi Kwankwaso tsantsar sahihiyar akidar siyasa ta gaskiya, ya ma fi shi kawo aiyukan cigaba a Kano, amma bai raga masa ba. Rimi ne yana gwamna a Kano, yasa aka fitar da Kwankwaso karatu Kasar Birtaniya, amma a karshen lamari an rabu ne cikin mummunan yanayi na siyasa. Hakika akwai rashin-ta-ido, koko rashin sanin tarihi, har da wani dan kwankwasiyya zai rika hargowar wai an yi maigidansa butulci a siyasa.

Sauya shekar Abba Daidai Ce

Babu damar zurfafa bayanai saboda karancin shafuka, a takaice, mu kalli dalilan Abba K. Yusuf na barin jam’iyyar NNPP a wannan lokaci zuwa jam’iyyar APC. Wasu dalilan ba za su fadu duka yanzu ba, duk da haka, za mu dan shafo abubuwan ne sama-sama illa-iyaka. Majiyoyi ingatattu sun tabbatar da cewa, a zaben Shekarar 2027 maizuwa, Kwankwaso ba zai bai wa Abba takarar tsayawa gwamna a Kano ba, nan da kwanaki masu zuwa, za mu gabatar da dalilan Kwankwason na hana Abba takara.

Yanzu haka akwai hukunci da Kotun Koli za ta yi game da halascin jam’iyyar kanta ta NNPP tsagin Kwankwaso. Sanin kowa ne, yanzu haka jam’iyyar ta NNPP ta kasu ne zuwa gida biyu, akwai mai alamar kayan -dadi, da kuma mai alamar littafi. Bangaren da Abba Gida Gida yake, a na rade-radin nan gaba, ko da ya kai ga samun nasarar lashe zaben gwamna a karo na biyu, kotu na iya kwace zaben, a bai wa wanda ya yi na 2, saboda tsagin nasa ba shi ne halastaccen tsagi ba a idon shari’a. Farfesa Kamilu Sani Fagge ma ya yi irin wannan tsokaci. A wane dalili Abba zai tsaya tsakanin wannan rashin tabbas.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *