Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arzikin Teku Ta Kaddamar Da Sabuwar Fasaha Don Janyo Masu Zuba Jari
[ad_1]
Daga Bello Hmaza
Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arzikin Teku, ta kaddamar da wata sabuwar fasahar zamani, ta adana bayanai da kuma wani sabon tsarin kara inganta bin ka’ida, domin kara ciyar da fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasa gaba.
Tsarin wanda a turance ake kiransa da ECMS, Ministan Ma’aiktar Adegboyega Oyetola, ne ya kaddamar da shi a Abuja, tare da marawar shugaban ma’aikata ta tarayya Didi Walson-Jack.
- Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi
- Gwamnan Gombe Ya Kafa Hukumar Kula Da Wutar Lantarki
Adegboyega a jawabinsa a wajen kaddamar ya sanar da cewa, sabuwar fasahar za ta taimaka matuka wajen kara karfafa adana bayanai da kara daukar matakai da kara taimaka wa ma’aikatasa wajen janyo msu zuba jari da kuma kara ingnta ayyukan ma’aikatar.
Ya bayyana cewa, sabuwar fasahar, ta yi daidai da ajandar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan samar da sauye-sauye ga tattali arzikin kasar nan.
Ya kara da cewa, tabbatar da ana bin ka’ida da gudanar da ayyuka kan lokaci, abu ne da zai kara karfafa zuba jari, na dogon zango ga bangaren tattalin arzikin kasar.
Kaddamar wadda ta gudana a taron karshen shekarar 2025 na ma’aikatar, ya samu halatar masu ruwa da tsaki,a fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar.
Ya ci gaba da cewa, kwaliya ta fara biyan kudin Sabulu, biyo bayan sauye-sauyen da ma’aikatar ta samar ga fannin, musamman duba da yadda aka samu karin ci gaba a sufurin fitar da Kifi, zuwa ketare da sauransu.
Ita kuwa shugabar ma’aikata ta tarayya Walson-Jack a na ta jawabin a wajen kaddamawar ta sanar da cewa, sabuwar fasahar za ta taimaka wajen rage samun jinkirin gudanar da ayyuka.
[ad_2]
Source link