Gwamnan Bauchi 2027: Kungiya Ta Fara Nema Wa Farfesa Pate Kuri’a

[ad_1]

Khalid Idris Doya

Wata kungiya mai suna, ‘Professor Pate Grassroots Mobement’ ta fara shiga lungu da sako domin neman wa ministan lafiya, Farfesa Ali Muhammad Pate kuri’a gabanin zaben kujerar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2027.

Shugagan kungiyar, Nazeef Sa’id Wambai, a yayin taron tuntuba da neman goyon bayan al’ummar gundumar Makama Sarkin Baki, ya shaida cewar akwai bukatar jama’a su fito su kada kuri’a domin zaben shugaban da ya dace kuma ya cancanta a yayin zaben 2027 da ke tafe.

  • Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji
  • Bankwana Da 2025, Maraba Da 2026

Ya ce al’ummar karkara su na gayar bukatar kyakkyawar shugabanci ta yadda za a samar musu da ababen more rayuka kamar su lafiya, tsaro, asibitoci, ruwa, hanyoyi da kuma kayan amfanin gona ba wai manyan motoci ko dima-diman gine-gine ba.

“Muna kan shiga kwararo-kwararo domin wayar wa jama’a kai dangane da ‘yancinsu kan yadda za su matsa kaimi wajen ganin an biya musu bukatunsu ta hanyar shiga a dama da su wajen zaban shugabannin da suka dace. Mun tattauna da kungiyoyin mata, maza, matasa, ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu wadanda matsalolin da ake fuskanta ya damesu kuma suke neman a kawo mai share musu hawaye.

“Sun shaida mana cewar babu ko asibiti guda daya a wannan gundumar. Kuma wannan gundumar na daga cikin manyan gundumomi a jihar Bauchi. Hakan na nuni da cewa suna zuwa wasu wuraren kenan domin neman lafiya. Muna son mu tunkari hukumomin da abun ya shafa kan wannan batun.”

Wambai ya ce Farfesa Muhammad Ali Pate a shirye yake wajen shawo kan matsalolin da suke addabar al’ummomin da suke jihar Bauchi wanda ke da kwarewa sosai a bangaren kiwon lafiya da sauran bangarori. Ya nemi al’ummar jihar da su mara wa Ali Pate baya a zaben 2027 domin ya kai ga shawo matsalolin da suke fuskantar jihar.

Daya daga cikin mazauna gundumar, Jamilu Aminu Gali, ya nuna aniyarsu na mara wa kungiyar baya, ya ce zauna da su domin jin matsalolinsu zai taimaka wajen ganin an kula da halin da suke ciki. Ya ce ba su da asibiti a gundumar hakan na janyowa suke shan wahala wajen daukan masu juna biyu zuwa asibitocin da ke kusa da su.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *