Sin Ta Jaddada Hadin Gwiwa Kan Sauyin Yanayi Da EU Inda Ta Lashi Takobin Daukar Matakai Kan Ka’idojin Cinikayya Na Rashin Adalci

[ad_1]

Kasar Sin ta bayyana cewa tana son yin aiki tare da Tarayyar Turai (EU) kan sauyin yanayi na duniya, amma kuma za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don mayar da martani ga duk wani takunkumin ciniki na rashin adalci. Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ce ta bayyana hakan a yau Alhamis, dangane da sabon tsarin daidaita matakin fitar da hayaki mai gurbata yanayi na EU mai lakabin CBAM.

Wani mai magana da yawun ma’aikatar ya ce EU ta yi watsi da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin samar da ci gaba mara gurbata muhalli ta hanyar sanya ka’idar kima mai tsanani game da fitar da hayakin carbon a kan kayayyakin kasar Sin a karkashin dokokin CBAM, wadanda aka tsara ci gaba da karuwarsu a kowace shekara nan da shekaru uku masu zuwa, inda ta ambaci matakan da “na rashin adalci” kuma “masu nuna wariya.”

A cewar mai magana da yawun ma’aikatar, “wannan bai yi daidai da gaskiyar abubuwan da ke gudana yanzu a kasar Sin da kuma yanayin ci gaban da za a samu a gaba ba”, yana mai nuni da cewa ana zargin dabi’un na EU sun karya ka’idodin hukumar cinikayya ta duniya (WTO) kuma sun saba wa ka’idar majalisar dinkin duniya ta manufa daya amma mai mabambantan hakkokin da suka kamata a sauke.

Tsarin na CBAM, wanda ya fara aiki a hukumance a yau Alhamis, mataki ne da EU ta dauka na shigar da farashin fitar da hayakin carbon a kan wasu kayayyaki masu fitar da hayakin da ke shiga kasashen EU, kuma masu samar da kaya na EU suka daidaita farashin na fitar da carbon a bangaren shigo da kaya da irin wannan fuskar a karkashin tsarin cinikayyar EU a bangaren fitar da hayaki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *