An kori Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano
[ad_1]
Jam’iyyar NNPP ta sanar da korar shugabanta na Jihar Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa, kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Rikicin NNPP ta ɗauki sabon salo ne a daren ranar Litinin, inda shugabanni jam’iyyar a Mazaɓar Gargari da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, suka sanar da korar Hashimu Suleiman Dungurawa daga Jam’iyyar.
Taron, ƙarƙashin jagorancin shugaban mazaɓar, Shuaibu Hassan, ya kori Hashimu Suleiman Dungurawa ne bisa zargin sa da haddasa rikicin da a halin yanzu yake gwara kan ’yan jam’iyyar, musamman tsakanin magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wannan ya zo ne yan sa’o’i bayan ɓullar batun shirin sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa Jam’iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna, duk da cewa kawo yanzu bai ce uffan ba a kan lamarin, ya riga ya shirya komawa APC, ko da kuwa Kwankwaso bai amince ba.
Batun sauyin sheƙar yana gwara kan ’yan NNPP, inda magoya bayan Abba ke neman ya jagorance su zuwa Jam’iyyar APC, a yayin da mabiyan madugu kuma uban gidansa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke adawa da hakan.
Tuni da shugabannin ƙananan hukumomi da kwamishinoni da hadiman gwamnan suka bayyana goyon bayansu ga sauyin sheƙar, wanda suka bayyana a matsayin alheri. Hakazalika ’yan majalisar dokokin jihar, in banda mutum uku.
Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a gidan Kwankwaso, ya ce bai ga dalilin sauya sheƙar ba, amma duk wanda ke son bin Abba zuwa APC na da ’yancin yin haka.
Sai dai kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga, wanda shi ne kaɗai sanatan NNPP a Najeriya, ya soki batun sauyin sheƙar a matsayin cin amana.
Sanata Hanga ya bayyana cewa duk masoyin Abba ba zai ba shi shawara ya yi wa Kwankwaso butulci ba, balle har ya koma APC.
A cewarsa komawa APC cin amanar talakawa ne, musamman a wannan hali na matsin rayuwa da jam’iyyar ta jefa talaka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link