Sauya sheka: Ba ma goyon bayan maciya amana — Sanata Hanga
[ad_1]
Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga ya yi watsi da rahotannin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, yana mai cewa ’yan Kano ba sa goyon bayan cin amana kuma ba za su bi shugabannin da suka yi watsi da amanar talakawa ba.
A cikin wani sauti da walikinmu ya samu, Sanata Hanga ya bayyana jita-jitar sauya sheƙar a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira don haifar da ruɗani da rikicin siyasa.
Ya ce masu yaɗa irin wannan magana ba su da gaskiya kuma ba su da kishin ƙasa.
Ya jaddada cewa babu magoyin bayan gaskiya da zai so Gwamna Abba ya ci amanar talakawan Kano da sauran al’ummar ƙasa ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki sakamakon cire tallafin mai da shirin ƙarin haraji.
Sanata Hanga ya tambayi dalilin da zai sa gwamnan zai bar NNPP, yana mai cewa APC ba ta da abin da za ta bayar da ya fi jam’iyyar da talakawa suka runguma.
Ya ce, “Idan ya koma APC, yaya talakawa za su bi shi zuwa jam’iyyar da ta jefa su cikin wahala? Yaya za a sake tsara ’yan majalisa da ’yan takara saboda son rai na mutum ɗaya?”
Sanatan ya ƙara da cewa rahotannin ƙarya ne da aka ƙulla don tayar da zaune tsaye, kuma har yanzu ba a sanar da shi game da wani shiri na sauya sheƙa daga bakin gwamna kansa ba.
Ya ce, “Ba ma son cin amana a Kano. Ba ma tafiya da marasa amana, kuma ba ma goyon bayan masu cin amana.”
Dangane da zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin tura gwamna zuwa APC, Hanga ya yi watsi da hakan, yana mai cewa wannan magana ta raina ƙwarewar Kwankwaso a siyasa.
Ya ce, “Jagora na nufin wanda ke gaba. Ba ya tura wani ya fara sauya sheka sannan ya bi shi daga baya.”
Hanga ya kuma bayyana cewa duk da wasu ’yan Majalisar Tarayyar da na jihar sun nuna niyyar bin gwamna zuwa wata jam’iyya, shi a matsayinsa na Sanatan NNPP, ya ƙi karɓar tayin kuɗi mai tsoka da aka yi masa don sauya sheƙa.
Ya ce irin waɗannan tayin ba su da amfani ga talakawa, kuma al’umma ba wauta ba ce da za a iya jan su bayan shugabanni sun karɓi biliyoyin naira.
Sanatan ya jaddada, “Ni ina tare da Kwankwaso ɗari bisa ɗari. Aƙidarsa ita ce hanya mafi inganci ga ci gaban jihar da ƙasa. Ba zan ci amanarsa ba, in sha Allah, har zuwa mutuwa.”
Ya yi kira ga magoya bayansa da kada su rikice, yana mai tunatar da su irin wahalar da suka sha a ƙarƙashin mulkin APC.
Ya ce, “Mutanenmu masu hankali ne. Duk wanda ya sauya sheka daga cikin shugabanni ya tafi shi kaɗai; talakawa ba za su bi shi ba.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link