Tsaro: Yadda Gwamnoni Ke Kafa Rundunonin Tsaro A Jihohinsu
Kalubalen tsaro a duk fadin Nijeriya, ba wani abu ba ne sabo, sai dai addu’ar Allah ya kawo sauki.
Masu sharhi kan harkokin tsaro, na fashin baki da cewa, gwamnatin tarayya na yin iya kokarinta amma akwai bukatar ta sauya dabarun yaki da masu aikata muggan laifuka da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, ra’ayin riƙau, safarar miyagun kwayoyi da dai sauransu.
- Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Kammala Zaman Zaunannen Kwamitinta
- An Samu Manyan Nasarori A Kannywood A ‘Yan Shekarun Nan –Maryan CTB
A yunƙurin da ake yi na ganin an shawo kan ƙalubalen tsaro, wasu gwamnoni a Kudanci da Arewacin Nijeriya, sun fara kaddamar da rundunar tsaro karkashin ikonsu don karfafa jami’an tsaro da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya wajen shawo kan ƙalubalen tsaro da ya dabaibaye sassan ƙasar.
A makon da ya gabata, gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rundunar tsaro wacce za ta sanya ido kan al’ummomin jihar a ranar Talata, 23 ga watan Disamba, 2025 a filin wasa na Sani Abacha, Kano.
Sabbin rundunar da aka kafa sun kunshi jami’ai 2,000 da aka zaƙulo a kananan hukumomi 44 na jihar, ciki har da mata 130 da maza 1,870, domin karfafa tsaro da tattara bayanan sirri a jihar.
Gwamna Yusuf ya sanar da cewa, za a samar wa rundunar kayan aiki isassu yadda za ta kasance cikin shiri don tunkarar masu aikata manyan laifuka, ciki har da fashi da makami, ta’ammuli da miyagun kwayoyi, ‘yan daba, da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron jama’a a birane da karkara.
A wannan rana, takwaran Gwamna Yusuf na jihar Filato, a wani sabon yunkuri na ƙarfafa yanayin tsaro domin samar da ingantacciyar zaman lafiya a faɗin Jihar, Gwamnan Caleb Manasseh Mutfwang, ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, yana mai bayyana tsaro a matsayin “tushen da ake gina ci gaba mai ɗorewa a kai.”
Gwamna Mutfwang ya yi wannan sanarwar ne a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, a filin wasa na Zaria Road, Jos, yayin bikin yaye jami’an rundunar tsaro mai suna ‘Rainbow’ su 1,450, da ke da alhakin taimakawa harkokin tsaron jihar domin fatattakar masu aikata muggan laifuka da ‘yan ta’adda dake addabar al’ummar jihar.
In ba a manta ba, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kaddamar da rundunar kare al’umma (CPG), wadda aka fi sani da Askarawan Zamfara. Wannan wani gagarumin ci gaba ne wajen magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta
Askarawan su 2,645 an ya ye kashin farko ne a 1 ga Fabrairun, 2024.
Har ila yau, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, a ranar Talata, 10/10/2023 ya kaddamar da rundunar kula da al’umma don karawa kokarin manyan hukumomin tsaro karfi a yaki da ‘yan fashi da makami a jihar.
Yayin da yake kaddamar da rukunin farko na rundunar, Radda ya ce hakan wani ɓangare ne na kokarin gwamnatinsa na daukar hanyar haɗa hannu da al’umma don magance rashin tsaro a jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula, ya fitar, rukunin farko na rundunar ya kunshi matasa 2,400 da aka zaba daga kananan hukumomi 34 na jihar.
Bugu da kari, akwai wata rundunar tsaro ta hadin gwiwa mai suna Amotekun – wata runduna ce ta tsaro ta yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya, wadda jihohin Yarbawa shida (Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Ekiti, Osun) suka kafa don magance matsalar rashin tsaro kamar garkuwa da mutane, da fashi da makami, da kuma kare manyan hanyoyi/dazuzzuka.
An ƙaddamar da ita a watan Janairun 2020, kuma ita ce runduna ta farko ta tsaro a yankin Nijeriya, wacce aka kafa a Ibadan, Jihar Oyo.
Wannan yunkurin da gwamnonin jihohi ke yi wurin ganin an kawo karshen taɓarɓarewar tsaro da ya baibaye kasar, na nuna cewa, lallai Akwai buƙatar sojoji da ‘yansanda su sauya dabarun yaki da masu aikata manyan laifuka, musamman ‘yan bindiga dake kashe al’umma ba tare da wani dalili ba.