Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Ta Farko Game Da Tattalin Arziki Mai Alaka Da Yanayin Duniyarmu
[ad_1]
Hukumar kula da harkokin yanayin duniyarmu ta kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da tattalin arziki mai alaka da yanayin duniyarmu, wadda ta kasance irinta ta farko a kasar. Takardar ta yi nazari a kan yadda za a sanya abubuwan da suka shafi yanayin duniyarmu su taimaka ga bunkasar tattalin arziki.
Takardar ta mayar da hankali a kan fannonin noma, da makamashi, da yawon shakatawa, da kiwon lafiya, da rage fitar da hayakin Carbon mai gurbata muhalli da sauransu, kuma ta hanyar nazarin abubuwa na zahiri, ta samar da tallafi ta fannin kimiyya ga bunkasar tattalin arziki, da kiyaye muhalli, tare da bayar da shawarwari ga gwamnati, wajen yanke shawara da kuma kulawa da harkokin yanayin duniyarmu.
Takardar ta kuma yi nazarin hanyoyin da za a bi wajen sa abubuwa masu alaka da yanayin duniyarmu, su taimaka ga bunkasar tattalin arziki. Misali, ta fannin aikin noma, tantance yanayin duniyarmu zai taimaka ga samar da isashen abinci. Ta fannin makamashi kuma, kara ingancin aikin hasashen yanayin duniyarmu zai kai ga rage hasarori a sanadin bala’u daga indallahi. Sai kuma, ta fannin yawon shakatawa, kyakkyawan yanayi irinsu gajimare masu tarin yawa, da fitowar rana da ke janyo masu yawon shakatawa, sun zamanto sabbin fannonin dake ingiza bunkasar tattalin arziki.
[ad_2]
Source link