Kwamitin majalisa ya kusa kammala binciken dokokin haraji




Kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincike kan zargin yi wa Dokokin Haraji cushe, ya bayyana cewa zai kammala aikinsa kuma ya gabatar da rahoto nan ba da dadewa ba.

Kwamitin, karkashin jagorancin Muktar Aliyu Betara (Borno, APC), ya yi taro na farko a ranar Talata, 23 ga watan Disamba, bayan wani dan majalisa ya nuna damuwa kan zargin wasu sauye-sauye da aka samu kan dokokin haraji da majalisar ta amince da su.

A yayin taron, mambobin sun yanke shawarar kammala binciken cikin sauri don kare doka, tabbatar da bin tsarin doka, da kuma karfafa amincewar jama’a da aikin majalisar.

Betara, ya tabbatar da cewa za su gabatar da sakamakon binciken da shawarwarin kwamitin nan ba da jimawa ba.

An kafa kwamitin mai mutum bakwai ne domin duba dokokin harajin da aka amince da su, ko sun yi daidai da wadanda aka fitar a hukumance, bisa tsarin kundin tsarin mulki da ka’idojin majalisa.

Dokokin harajin sun hada da: Dokar Kafa Hukumar Kula da Haraji ta Kasa (National Revenue Service Establishment Act), Dokar Kafa Hukumar Hadin Gwiwar Haraji ta Najeriya (Joint Revenue Board of Nigeria Establishment Act), Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya (Nigeria Tax Administration Act), da Dokar Haraji ta Najeriya (Nigeria Tax Act).

Dokokin sun samu amincewar a dukkanin majalisun biyu a watan Maris, sannan Shugaba Bola Tinubu ya sanya musu hannu a watan Yuni, sannan aka fitar da su a hukumance a ranar 26 ga watan Yuni.

Hon. Abdulsammad Dasuki ne, ya fara zargin akwai cushe a cikin dokokin, wanda hakan ya sa aka kafa kwamiti don yin bincike.

Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 27 ga watan Janairu, 2026, saboda bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *