’Yan majalisa da dama sun yi watsi da sauye-sauyen dokar harajin Tinubu
[ad_1]
Wasu daga cikin ’yan Majalisar Tarayya sun nuna damuwa cewa sabbin dokokin haraji ba su yi daidai da waɗanda Majalisar Ƙasa ta amince da su ba.
Batun ya fara ne bayan wani ɗan majalisa, Abdulsammad Dasuki, ya zargi cewa dokokin harajin da aka fitar sun ƙunshi sauye-sauyen da ba a tattauna ko amince da su a majalisa ba.
Ya ce hakan ya saɓa wa tsarin dokoki tare da haifar da damuwa game da kundin tsarin mulki.
Wasu ’yan majalisa biyu, Muhammad Bello Fagge da Yusuf Shitu Galambi, sun goyi bayan wannan zargi, inda suka yi gargaɗin cewa irin waɗannan sauye-sauyen na iya raunana dimokiraɗiyya da rage amincewar jama’a ga gwamnati.
“Abin da ke ciki ba shi ne abin da muka tattauna kuma muka amince da shi a Majalisar Ƙasa ba,” in ji Fagge.
“Ko da sashe ɗaya ne kawai ya bambanta, hakan babbar matsala ce.”
Sun ce wasu sassa na dokokin na nuna an bai wa ɓangaren zartarwa, musamman Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa, fifiko fiye da ƙima ba tare da isasshen sanya ido daga majalisa ko kotuna ba.
Galambi, ya yi kira da a dakatar da aiwatar da dokokin harajin, waɗanda aka shirya fara amfani da su a watan Janairun 2026, har sai kwamitin Majalisar Wakilai ya kammala bincikensa.
“Idan an gano an sauya dokokin, dole a gyara su, su dace da abin da ’yan majalisa suka amince da shi. Idan ba haka ba, to a ci gaba da aiwatarwa,” in ji Galambi.
Masana kuma sun yi gargaɗin cewa sauya dokoki bayan an amince da su na iya zama barazana ga tsarin mulki da ƙara rage amincewar jama’a.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce sabbin dokokin harajin adalci ne, suna kare haƙƙin masu biyan haraji.
A cewar gwamnatin, za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi, inda ta ƙara da cewa an soke wasu haraji domin rage wa ’yan Najeriya wahalhalu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link