Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce taɓarɓarewar rashin tsaro a Najeriya na nuna gazawar shugabanci.
Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi cikin gaggawa kan zargin wasu jami’an gwamnati da taimaka wa ’yan ta’adda.
Obi, ya bayyana hakan ne bayan wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, inda wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka ce jami’an gwamnati ne ke taimaka musu da makamai.
Ya ce wannan zargi abu ne mai matuƙar muhimmanci da bai kamata a yi watsi da shi ba.
“An ga wani bidiyo mai tayar da hankali a Jihar Kwara inda waɗanda aka kama suka ce jami’an gwamnati ne suka ba su harsasai da kayan aiki.
“Wannan zargi na buƙatar bincike cikin gaggawa kuma a bayyane.”
Obi ya ce duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe a fannin tsaro tsawon shekaru, rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
“An kashe tiriliyoyin juɗi da biliyoyin daloli a fannin tsaro, amma duk da haka rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ba a amfani da na’urorin zamani da fasahar tsaro wajen gano da kama ’yan ta’adda, duk da cewa ƙasar na da irin waɗannan damarmaki.
“Gwamnati na da iko da hanyoyin sadarwa, bayanan sirri da bin sahun kuɗaɗe, amma duk da haka satar mutane da ta’addanci na ci gaba da ƙaruwa.”
Obi ya kuma soki yadda ake murnar sakin waɗanda aka sace ba tare da kama waɗanda suka aikata laifin ba, inda ya ce hakan na nuna rashin ɗaukar al’amarin da muhimmanci.
A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin tsaro na nuni da gazawar gwamnati da kuma yin sakaci, inda ya jaddada cewa babban aikin kowace gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link