Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
[ad_1]
Dakarun Sojin Operation HADIN KAI sun daƙile wani hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansanin soji na Mairari da ke Jihar Borno.
Harin ya fara ne daga daren ranar Juma’a zuwa safiyar Asabar.
A cewar rundunar, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin shiga sansanin ta hanyar amfani da motoci biyu da suka cika su maƙil abubuwan fashewa.
Jami’in yaɗa labarai na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce sojoji sun gano motocin kuma suka tarwatsa su kafin su kai ga shiga sansanin.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka jikkata.
Waɗanda suka tsira sun kwashe gawarwaki da waɗanda suka ji rauni a wajen bayan tafka artabu.
Bayan daƙile harin, sojoji tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun gudanar da bincike a yankin.
A yayin binciken, sun gano gawar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da kayayyaki da dama da suka bari.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi, harsasai, gurneti, babura, na’urorin sadarwa, kayan yaƙi, da kayayyakin jinya.
Laftanar Kanal Uba, ya ce ƙwato waɗannan kayayyaki ya rage ƙarfin ’yan ta’addan da ikonsu na ci gaba da kai hare-hare a yankin.
Ya ƙara da cewa dakarun sun lalata motocin da aka maƙare da kayan fashewa, wanda ya jawo lalacewar wasu wurare biyu, amma ba su yi nasarar shiga sansanin sojin ba.
Ya ce a halin yanzu sojoji na ci gaba da yin sintiri domin hana sake kai hare-hare tare da bai wa al’ummar yankin tabbacin tsaro.
Rundunar sojin ta jaddada ƙudirinta na kawar da ’yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link