Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
[ad_1]
Mai horar da Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya ce zai sanya Mohammed Salah cikin jerin ’yan wasan da za su buga wa Liverpool wasa da Brighton a ranar Asabar.
Slot wanda ya samu saɓani da Salah kan ajiye shi a benci a wasanni uku a jere, ya ce yana da yaƙinin cewa, Salah zai ci gaba da bugawa ƙungiyar wasa.
Ya kuma ƙara da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan domin ya ci gaba da taka leda a Anfield.
Salah mai shekara 33, baya cikin jerin ‘yan wasan da suka doke Inter Milan a Italiya a ranar Talata, wanda hakan ke bayyana tsamin rashin jituwa tsakaninsa da Arne Slot.
Liverpool dai zata karɓi baƙuncin Brighton a wasan mako na 16 da ƙarfe 3 na ranar Asabar.
Mo Salah, ɗan asalin ƙasar Masar, ya bugawa Liverpool wasanni 420 tare da zura ƙwallaye 250 cikin zamansa a ƙungiyyar.
Ɗan wasan zai bar Liverpool domin dawowa ƙasar Masar a ranar 15 ga watan Disamba, kwanaki 6 gabanin fara kofin nahiyyar Afrika da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link