Za Mu Fara Amfani Da Jirage Marasa Matuƙa Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta sayi jirage marasa matuƙa da sauran kayan aiki don inganta tsaro a yankunan da ke iyaka da Kano da Katsina bayan hare-haren ’yan bindiga a yankunan.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanonin rundunar JTF a Tsanyawa da Shanono.

A cewar mai magana da yawunsa, jirage  za su taimaka wajen tattara bayanan sirri da saurin ɗaukar mataki kan barazanar tsaro.

Gwamnan ya roƙi jama’a su riƙa ba da rahoton duk wani abu da suka gani da ya shafi motsin ’yan bindiga.

Ya kuma ce Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin bayar da tallafi bayan sanar da shi halin da ake ciki.

Gwamnan ya tabbatar wa jama’a cewa za a ceto waɗanda aka sace a yankin.

Kimanin mutane biyar aka sace a Tsanyawa da kuma mutane 10 a Shanono.

Ya ce waɗannan hare-hare ba su saba faruwa a Kano ba, kuma gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *