An ceto mutane 26 ana neman 25 a Sakkwato
[ad_1]
Kawo yanzu an ceto mutum 26 ana ci gaba da neman wasu 25 bayan hatsarin kwalekwale a yankin Goron yo da ke Jihar Sakkwato.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sanar da cewa irgin ruwan ya dauko mutane 51 tare da kayansu da babura kafin ya tuntsure.
Babban Jami’in Kula da Ayyukkan na Hukumar, Aliyu Shehu ya bayyana cewa “Kokarin ceto mutanen na tafiya kuma mun sanar da garuruwa makwabta su taimaka a wajen bincikar mana mutanen a wurin da suke.”
A lokacin da manema labarai suka tafi wurin dangin wadanda suka nutse, sun yi jungum don rashin tabbas ga ’yan uwansu.
Jami’ai daga Hukumar Kula da Gulabe ta Kasa (NIWA) sun tafi wurin, inda Manajan yanki, Injiniya Muhammad Bala ya nuna rashin jin dadin hukumar kan hatsarin.
Ya yi kira ga matuka jirgi su rika kula da ka’idar tuki su daina daukar fashinja da yawan da ya wuce kima.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link