Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo

[ad_1]



Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya na buƙatar taimakon ƙasashen waje don dakatar da kashe-kashe da rashin tsaro, domin gwamnati ta gaza kare al’umma.

Ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana Jihar Filato, inda ya ce a ci gaba ya kawo fasahar da za a iya gano masu aikata laifi, amma ta gaza yin hakan.

Obasanjo, ya yi gargaɗin cewa ana kashe ’yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba, don haka gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki.

Ya ce idan gwamnati ta kasa kare jama’a, ’yan ƙasa na da damar neman taimakon ƙasashen duniya.

Ya soki masu kare kashe-kashen da ake yi, inda ya bayyana cewa rayuwar kowanne ɗan Najeriya na da muhimmanci.

Obasanjo, ya kuma tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke tattaunawa ko biyan kuɗin ’yan bindiga kuɗin fansa, inda ya ce hakan na ƙara taɓarɓarewar lamarin.

Ya kira ’yan Najeriya da su haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa kowa na rayuwa ba tare da fargaba ba.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, shi ma ya yi jawabi a wajen taron.

Ya ce al’ummar jihar dole su haɗa kai su daina abubuwan da za su raba su.

Mutfwang, ya buƙaci jama’a su yi aiki tare domin jihar ta ci gaba da kuma shawo kan matsalolin tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *