Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Ga Babban Taron Ranar Nuna Goyon Baya Ga Palasdinawa Ta Duniya
[ad_1]
Ranar 25 ga wata, an gudanar da babban taron ranar nuna goyon baya ga Palasdinawa ta duniya a MDD. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aika da sakon taya murna ga babban taron.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, batun Palasdinu, muhimmin bangare ne na sha’anin yankin Gabas ta Tsakiya, da ya shafi nuna gaskiya da adalcin duniya, da kuma yin tasiri ga yanayin da yankin ke ciki.
A halin yanzu kamata ya yi kasashen duniya su kara cimma daidaito da daukar matakai cikin himma, a kokarin tabbatar da tsagaita bude wuta na har abada a baki dayan zirin Gaza da kuma hana sake barkewar yake-yake. Haka kuma wajibi ne a bari Palasdinawa su tafiyar da harkokinsu da kansu bayan yakin, da sake gina zirin, a kuma mutunta burin Palasdinawa, tare da magance damuwar kasashen da ke yankin.
Har ila yau wajibi ne a gaggauta warware matsalar jin kai a zirin Gaza, a rage wahalhahun da Palasdinawa suke fuskanta. Abu mafi muhimmanci shi ne bin turbar manufar kafa kasashe 2, a kokarin warware batun Palasdinu a siyasance cikin hanzari.
Haka zalika, Xi ya jaddada cewa, batun na Palasdinu wata jarrabawa ce ga yadda ake jagorancin duniya yadda ya kamata. Kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su daidaita ainihin dalilin da ya haddasa lamarin, su sauke nauyin da ke wuyansu, su dauki matakai masu amfani, su gyara kuskure, su kuma kiyaye adalci da gaskiya.
A matsayin kasa mai kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin na tsayawa ga goyon bayan sha’anin adalci na maido da halastattun hakkokin al’ummar Palasdinu. Kuma za ta ci gaba da hada kai da kasashen duniya wajen daidaita batun na Palasdinawa daga dukkan fannoni cikin adalci da hanzari. (Tasallah Yuan)
[ad_2]
Source link